Shin ankama ma’aiktan hukumar dakile yaduwar cututtuka ta kasa NCDC suna masha’a?

Tantancewar CDD: Karya Ne!

Tushen Magana:

A ranar 1 ga watan  Yulin da muke ciki ne masu tantance sahihancin labarai na CDD mutane suka rika aikowa CDD wani bidiyo ta manhajar WhatsApp dan neman CDD din ta bincika musu gaskiyar al’amarin.

Bidiyon wanda aka yimasa taken: “ma’aikatan NCDC a daya daga cikin wuraren killace mutane suna aikata masha’a ba tare da sanin cewa na’ura tana nadan abinda suke aikatawa ba”.

Gaskiyar Magana:

Mutanen da suke cikin wannan bidiyo da ake aikata masha’a ba ma’aikatan hukumar dakile yaduwar cututtuka ta kasa NCDC bane.

Acikin bidiyon anga mace da namiji kansu a rufe kuma cikin shigar samun kariya daga cuta suna aikata badala.

Binciken da CDD ta gudanar da gano cewa bidiyon ya samo asaline daga kasar Kenya amma ba Najeriya ba, dan haka bashi da wata alaka da kowace wajen killace mutane acikin Najeriya ko ma’aiaktan hukumar NCDC.

Tun farko dai kafar sadawar Opera News Hub c eta wallafa labarin inda tace a ranar  25 ga watan Yunin wannan shekera ne wannan abu ya inda wassu ma’aurata biyu dake aiki wa wani kantin sayar da abinci suka yi wannan masha’ar.

Wannan bidiyo da aka yadashi sosai yaja hankali musamman a kasar Afrika Ta Kudu ina mutane da yawa sukayi ta kira-kirayen neman a hukunta wadannan ma’aikata.

A martanin da ya mayar, kantin sayar da abincin yace lallai zai hukunta wadannan ma’aikata nasa bisa wannan danyen aiki bayan ya ya umurci sashin sa mai kula da saita al’amura day a cire wannan faifan bidiyo day a janyo cece-kuce.

Itama a martaninsa game da batun, Dr. Chinwe Ochu wanda itace shugaban sashin dake kula da yaduwar cututtuka da alkinta dabaru na hukumar NCDC tace aikin NCDC shine jagoranci akan abinda ya shafi annoba da take da alaka da lafiya a matakin tarayya.

Ochu ta kara da cewa: “kodayake hukumar NCDC tana tallawa jahohi wadan da sune ke jagorantar al’amura a jahohin su daban-daban, NCDC tana maida hankali ne akan lafiyar amma ba abinda ya shafi kula da wuraren killace mutane ba dama lamarin marasa lafiya da ma’aikatan lafiya ba balata na yadda abubuwa suke wakana a wajen killace mutane”.

Kammalawa:

Wani bidiyo da ake yadawa tare da wani labari dake cewa ankama ma’aikatan hukumar NCDC suna aikata badala a wani wajen killace mutane karya ne. Wannan al’amari ya faru a kasar Kenya inda wassu ma’aikatan wani kantin sayar da abinci suka aikata wannan badala.

CDD tana jan hankalin mutane da su guji yada labaran da basu da tabbas akansu. CDD har wayau na jan hankalin jama’a das u daina karanta jigon labari kawai, amma su rika karanta gundarin dan fahimta ina ya dosa.

#AdainaYadaLabaranKarya

Leave a Comment

Your email address will not be published.