Shin an Yankewa Rahma Sadau Hukuncin Kisa Sakamakon Janyowa Addinin Musulunci Batanci?

Gaskiyar Magana: Karya Ne!

Tushen Magana: a ranar Talata, 10 ga watan Nuwanban shekara ta 2020, masu tantance sahihancin labarai na Cibiyar Bunkasa Demokaradiyya da Cigaba (CDD) sun gano wani labarai da majiyoyi da yawa suka wallafa shi. Labarin yace an yankewa sananniyar mai taka rawa a fina-finai, Rahma Sadau hukuncin kisa bisa janyowa addinin Musulunci maganganun batanci.

Labarin yace hukuncin kisan ya biyo bayan hotuna ne da Rahman ta wallafa wadan da ke nuna gadon bayan a fili kuma suka janyo cece-kuce musamman a yankin arewacin Najeriya dama Musulman yankin.

Majiyoyin da suka wallafa labarin sun hada da: Zazzau 2TV, Murna Hausa Top TV, Hausa Blog TV, MNS TV, Celebrities Buzz, Nairaland, Flip TV, LUS Entertainment, Gossip, Omokoshaban da lfy.

Wassu daga cikin majiyoyin sunce Shugaba Muhammadu Buhari ya amince da hukuncin kisan akan Rahma Sadau din.

Gaskiyar Magana:

Binciken da CDD ta gudanar ya gano cewa kawo lokacin hada wannan rahoto (13 ga Nuwanba, 2020) ba’a yankewa Rahma Sadau hukuncin kisa ba, duk kuwa da cewa majiyoyi da dama sun rawaito hakan.

A ranar 2 ga watan Nuwanban shekara ta 2020, Rahma Sadau ta wallafa hotuna masu nuna tsaraicin ta a shafukan sada zumunta da muhawara. Hotunan wadan da aka yada su musamman a Facebook da Instagram da Twitter da WhatsApp sun nuna gadon bayan Rahma a fili, al’amarin day a fusata Musulmai da yawa daga areewacin Najeriya.

Bayan wallafa wadan nan hotuna da cece-kucen da suka janyo an samu wani mutumin da yayi katobara da kalaman batanci akan Manzon Tsira Annabi Muhammadu (S.A.W), wannan lamari ya fusata dukkan Musulmai matuka-gaya.

Bayan faruwar lamarin ne akaga Rahma Sadau acikin wani bidiyo inda cikin zubda hawaye ta baiwa al’ummar Musulmai hakuri tana mai bayyana takaici da nadamar ta game faruwar lamarin.

CDD ta tabbatar da cewa kawo ranar 13 ga watan Nuwanba, 2020 babu wani hukuncin kisa da aka yankewa Rahma Sadau.

Kammalawa:

Ba’a yankewa Rahma Sadau hukuncin kisa ba sakamakon janyo wa addinin Musulunci batanci. Hakanan labarin da ake yadawa cewa Shugaba Muhammadu Buhari ya amince da yanke hukuncin kisa akan Rahman karya ne.

CDD tana jan hankalin jama’a game da yada labaran da basu da tabbacin sahihancin su. Kuna iya aikowa CDD labaran da kuke shakku akansu dan tantance muku ta hanyar WhatsApp ko gajeren sako ta wannan lamba +2349062910568 ko a shafin Twitter a: @CDDWestAfrica ko @CDDWestAfrica_H

#AgujiYadaLabaranBogi

Center for Democracy and Development West Africa| CDD West Africa