Shin An Samu Rudani a Garin Legos Sakamakon Raba Rigakafin Cutar Korona?

Gaskiyar Al’amari: Karya Ne!

Tushen Magana:

A ranar Ladi, 31 ga watan Janairun shekara ta 2021, masu bin diddigin labarai dan gano gaskiyar su na Cibiyar Bunkasa Demokaradiyya da Cigaba (CDD) sun gano wata murya mai tsawon dakika 51 da aka nada cikin harshen Hausa kuma ake yadawa ta manhajar WhatsApp. Muryar na cewa an samu hargitsi a garin Lagos inda mutane ke ta guduwa daga gidajen su, wasu ma na fadowa daga saman beni a yunkurin su na gujewa rigakafin cutar Korona da a cewar wannan murya ake rabawa a garin na Legas.

Wani sashi na sakon yace: “ana ci gaba da samun turmutsitsi a Legas sakamakon raba rigakafin cutar Korona”

“Turawa ne suka kirkiri rigakafin kuma lokacin da aka gwada shi akan mutane 1000 a kasar Birtaniya, 600 daga cikin wannan adadi sun mutu, wannan shine dalilin da yasa suke so su gwada akan bakaken fata. Allah ya kare mu”, inji wannan murya ta namiji da aka nada kuma ake yada ta ta manhajar WhatsApp.

Gaskiyar Magana:

Binciken da CDD ta gudanar game da maganar cewa mutane na gujewa rigakafin cutar Korona a jahar Legas ya gano cewa karya ne.

Hujjojin da CDD ta tattara sakamakon binciken da ta gudanar sun bayyana cewa har yanzu ba’a shigo da rigakafin cutar Korona kasar Najeriya ba, dan haka batun fara raba shi ko mutane a Legas na guje masa karya ne.

Har wayau, CDD ta gano cewa babu wani yanayi da ya shafi gujewa jami’an lafiya a jahar Legas saboda raba maganin cutar Korona da suke yi.

Jaridar AfricaNews ta rawaito babban daraktan hukumar lafiya a matakin farko na Najeriya, Dr. Faisal Shuaib na cewa za’a shigo da rigakafin cutar Korona guda 100,000 Najeriya a zangon farko a watan Fabrairun shekara ta 2021 wadda kanfanin sarrafa magani na Pfizer zai samar.

Dr. Shuaib ya kara da cewa: “za mu shigo da rigakafin cutar Korona wadda kanafanin Pfizer ya samar wadda ke bukatar sarrafawa a ma’aunin Celsius 70”.

Kammalawa:

Wata murya mai tsawon dakika 51 da aka nada kuma ake yadawa ta manhajar WhatsApp cewa mutane na gujewa rigakafin cutar Korona a garin Legas karya ne. Kawo lokacin hada wannan rahoto a ranar 1 ga watan Fabrairun shekara ta 2021 ba’a kawo rigakafin cutar Korona Najeriya ba balle ma ace mutane na guje masa a Legas sakamakon rabashi gare su. Wannan labari ne na bogi.

Al’amura na ci gaba da wakana lafiya kalau a Legas kuma mutane basu gujewa jami’an lafiya ba kamar yadda wannan sakon WhatsApp ya bayyana.

CDD na jan hanakalin jama’a da cewa su guji kirikira ko yada labarai ko sakonni na karya.

Kuna iya aikowa CDD labarai ko sakonnin da kuke da shakku akansu dan tantance muku sahihancin su ta wannan lamba +2349062910568, kuna ma iya aiko sakon WhatsApp.

#AgujiYadaLabaranKarya

Center for Democracy and Development West Africa| CDD West Africa