Shin an Rufe Asibitin Yara Na Khalifa Sheikh Isyaka Rabiu Dake Kano Sakamakon Samun Mai Dauke Da Cutar Corona?

Gaskiyar Magana: Karya Ne!

Tushen Magana:

A ranar Litinin, 14 ga watan Disamban shekara ta 2020 a yada wani labari acikin garin Kano, labarin yace an rufe Asibitin Yara na Khalifa Sheikh Isyaka Rabiu dake titin zuwa gidan Zoo sakamakon samun mai dauke da cutar sarkewar numfashi ta Corona.

Gaskiyar Magana:

Binciken da CDD ta gudanar ya gano cewa jita-jitar da ake yadawa cewa an rufe asibitin yara na Khalifa Sheikh Isyaka Rabiu dake titin Zoo road a birnin Kano bayan samu mai dauke da cutar Corona karya ne.

A ziyarar da mai binciken kwaf-kwaf dan gano sahihancin labara I na CDD yakai asibitin ya gano cewa komai yana tafiya dai-dai a asibitin, kuma marasa lafiya na ganin likitoci kamar yadda aka saba.

Hakanan jita-jitar da aka yada cewa an samu mai dauke da cutar Corona a asibitin karya ne.

Da CDD ta tuntube, shugabar asibitin, Dr. Hadiza Ashir asibitin yana cigaba da aiki kamar ya day a saba kuma babu wani mai dauke da cutar Corona da aka samu a asibitin, ta kara da cewa labarin cewa an rufe asibitin bayan bullar cutar COVID1-9 karya ne.

Shugabar asibitin ta kara da cewa basu san inda wannan labari na bogi ya bulla ba.

Dr. Hadiza tace: “nayi mamakin yadda mutane suka dinga kirana a waya suna tambaya ta game da bullar cutar Corona a asibitin, avind ya faru shine, ranar Ladi da daddare an kwao wata mata mai cutar ciwoan zuciya da hawan jinni wadda likita a asibitin, Dr. Adefemi ya bata kulawa.

“bayan kawo ta asibitin, an sanar da kwamitin kar ta kwana na jahar Kano kan cutar Corona kuma sunzo sun duba ta inda suka samfurin ta dan kaiwa dakin gwaje-gwaje amma matar ta mutu da yammacin ranar Litinin, ranar Litinin, 14 ga watan Disamba, 2020.

“a lokacin da ake fitar da gawar ta daga asibitin sai wani mutum ya fara daukan bidiyon motar dake dauke da ita, lokacin da yan uwanta suka gano shi sai hayaniya ta barke inda suka kwace wayar tare da dukan sa, lokacin da ake wannan turka-turka ne mutane suka taru inda masu gadin asibiitn suka rufe mashigar dan takaita shigar jama’a cikin asibitin”

Shima da aka tuntube shi, sakataren kwamitin yaki da cutar Corona na jaharr Kano, Dr. Imam Wada Bello yace labarin rufe asibitin yara dake titin gidan Zoo a Kano karya ne.

Dr. Imam yace: “asibitin yana aiki kamar yadda ya kamata kuma babu wanda ya rufe shi, dan haka mutane suyi watsi da labarin da ake yadawa cewa an rufe shi sakamakon samun mai dauke da cutar Corona”.

Kammalawa:

Labarin da ake yadawa cewa an rufe asibitin yara na Khalifa Sheikh Isyaka Rabiu dake Kano bayan samun mai dauke da cutar Corona karya ne, binciken CDD ya gano cewa ba’a rufe asibitin ba.

CDD na jan hankalin jama’a game yada labaran da basu tantance sahihancin su ba.

Kuna iya aikowa CDD labaran da kuke shakku akansu dan tantance muku ta hanyar WhatsApp ko gajeren sako ta wannan lamba +2349062910568 ko a shafin Twitter a: @CDDWestAfrica ko @CDDWestAfrica_H

#AgujiYadaLabaranBogi

Center for Democracy and Development West Africa| CDD West Africa