Shin An Nada Tsohon Sarkin Kano Sunusi Khalifan Shehu Tijjani Na Nahiyar Afirka?

Tantancewar CDD: Hakan Ba Gaskiya Bane!

Tushen Magana:

A ranar Litinin, 10 ga watan Agustan shekara ta 2020, masu tantance sahihancin labarai na Cibiyar Bunkasa Demokaradiyya da Cigaba (CDD) suka gano wani labari da ake yadawa shafuka sada zumunta na zamani, labarin yace an nada tsohon sarkin Kano, Malam Muhammadu Sunusi II a matsayi mikamin Khalifan Shehu Tijjani na nahiyar Afirka.

Kamar yadda labari ya zayyana, nadin Sarki Sunusi ya biyo bayan ziyarar ta’aziyya da yakaiwa Alan Sheikh Ibrahim Ilyasu a kasar Senegal ne.

Wata majiya mai suna Hausa Reporters ta rawaito cewa Tsohon Sarki Sunusi ya gaji kakansa ne bisa darewa kagarar mukamin Khalifan Shehu Tijjani na Afirka dama kasancewa Sarkin Kano.

Suma a nasu rahoton, Hausa Info da Opera News, sun rawaito cewa an nada Sarki Sunusi a mukamin Khalifan Shehu Tijjani na nahiyar Afirka.

Gaskiyar Magana:

A ranar 6 ga watan Agustan shekara ta 2020, Sarki Sunusi ya tashi zuwa kasar Senegal dan yiwa iyalan Sheikh Ibrahim Ilyasu ta’aziyya bisa rashi da aka yimusu.

Tantancewar da CDD ta aiwatar ta gano cewa ba’a nada Sarki Sunusi a mikamin Khalifan Shehu Tijjani na nahiyar Afirka ba, duk kuwa da cewa majiyoyi da yawa sun rawaito faruwar hakan, amma CDD ta gano cewa labari ne na bogi.

Da aka tuntube ta game da baton, mai taimaka Tsohon Sarki Sunusi a bangaren hulda jama’a da yada labarai, Maryam Hamisu tace nadin Sarkin a mukamin Khalifan Tijjaniyya na nahiyar Afirka bai tabbata ba.

Maryam ta kara da cewa: “muna haka kaga labarin a shafukan sada zumunta na zamani, amma gaskiyar magana itace, labarin labari ne na bogi”.

Kammalawa:

Labarin da ake yadawa cewa an nada Tsohon Sarkin Kano Sunusi a mukamin Khalifan Shehu Tijjani na nahiyar Afirka labari ne na bogi, hakan bata tabbata ba.

Kawo yanzu babu wata sanarwa da fito daga iyalan Sheikh Ibrahim Inyass dake bayyana nadin Khalifan Shehu Tijjani a Afirka.

CDD tana jan hankalin jama’a da suyi watsi da labarin nadin Khalifancin Tijjani na nahiyar Afirkan.

Kuna iya turo labaran da kuke da shakku akansu dan muyi muku binciken kwakwaf tare da tantancewa.


Ku kiramu akan lamba: +2349062910568 ko ku tuntube mu a shafin mu na Twitter a: @CDDWestAfrica ko @CDDWestAfrica_H

#AgujiYadaLabaranBogi.

Center for Democracy and Development West Africa| CDD West Africa

Leave a Comment

Your email address will not be published.