Shin an Nada Alhaji Mannir Jafaru a Matsayin Sabon Sarkin Zaria?

Gaskiyar Magana: Karya Ne!

Tushen Magana:

Labarai da rahotanni da ake yadawa a kafofin sada zumunta na zamani na cewa an nada Yariman Zazzau wato Alhaji Mannir Jafaru a matsayin sabon sarkin Zaria, kamar yadda labaran ke bayyanawa nadin Mannir Jafarun ya biyon bayan rasuwar marigayi sarkin Zaria, Alhaji Shehu Idris.

Wani hoto da ake ikirari ya fito daga shafin Gwamnan Kaduna Malam Nasir Elrufa’i ya nuna Alhaji Mannir Jafaru sanye da rawani inda rubutu dake saman hoton yace Elrufa’i ya amince da nadin Mannir Jafarun a matsayin sabon sarkin Zaria.

Hoton wanda masu tantance sahihancin labarai na Cibiyar Bunkasa Demokaradiyya da Cigaba (CDD) suka gani ya nuna cewa nadin sabon sarkin ya faru sakamakon rasuwar Alhaji Shehu Idris mai shekaru 84.

Ikirarin nadin Mannir Jafarun ya janyo cece-kuce musamman a shafukan sada zumunta na zamani inda mutane suka rika bada ba’asi game da labarin.

Gaskiyar Magana:

Binciken da CDD ta gudanar ya gano cewa labarin nada Mannir Jafaru a matsayin sabon sarkin Zaria karya ne. Hakanan hoton da aka yada da yayi ikirarin cewa ya fito daga shafin Twitter na gwamnan Kaduna Malam Nasir Elrufa’i hoto ne da aka kirkireshi da manufar yada labarin bogi kuma bai fito daga shafin Twitter na Elrufa’in ba.

Da CDD ta tuntube shi dan tantance gaskiyar lamarin, mai baiwa gwamnan Kaduna shawara akan harkokin yada labarai da sadarwa, Muyiwa Adekeye ya bayyana labarin a matsayin na bogi.

Muyiwa ya kara da cewa: “wannan labari ne maras tushe dake cike da karya, bayan addu’ar sadakar uku da akayi, yanzu aiki ya koma ga wadanda zaban sabon sarki ya rataya a wuyansu”.

CDD na kara tabbatar da cewa kawo lokacin rubuta wannan tantancewa ba’a nada Mannir Jafaru a matsayin sabon sarkin Zaria ba.

Kammalawa:

Labarin da ake yadawa cewa an nada Yariman Zazzau Alhaji Mannir Jafaru a matsayin sabon sarkin Zaria karya ne. kawo yanzu babu wata sanarwa daga gwamnatin Kaduna game da nada sabon sarkin. Duk labarai da bayanan dake yawo a shafukan sada zumunta na zamani labarai ne marasa tushe.

CDD tana kira ga jama’a da suyi watsi da labarin tare da dakatar da yadashi a dukkan kafafen sadarwa.

Kuna iya aikowa CDD labarai ko bayanan da kuke da shakku akansu dan ta tantance muku sahihancin su. Zaku iya turo labaran ta wannan lamba: +2349062910568 ko a shafukan mu na Twitter a @CDDWestAfrica ko @CDDWestAfrica_H

Center for Democracy and Development West Africa| CDD West Africa