Shin an Nada Ahmed Nuhu Bamalli a Matsayin Sabon Sarkin Zazzau?

Amsa: Eh, Gaskiya Ne!

Tushen Magana:

A ranar Laraba, 7 ga watan Octoban shekara ta 2020 masu tantance sahihancin labarai na Cibiyar Bunkasa Demokaradiyya da Cigaba (CDD) sun gano labarai da rahotanni dama hotuna da aketa yadawa a dandalin sada zumunta na zamani cewa an nada Alhaji Ahmed Nuhu Bamalli a matsayin sabon sarkin Zazzau.

Hotuna da labaran dad a yada a kafafen sada zumunta na zamani an yadasu ne tare da wasikar da take bayyyana nadin sabon sarkin wadda kwaminshinan kananan hukumomi na jahar Kaduna Ja’afaru Ibrahim Sani ya sanyawa hannu.

Gaskiyar Magana:

Rahotanni da labaran da ake yadawa cewa an nada Alhaji Ahmed Nuhu Bamalli a matsayin sabon sarkin Zazzau gaskiya.

Domin tantance sahihancin nadin Bamallin CDD ta samu kwafin wasikar da take bayyana nadin nasa wadda kuma aka wallafa ta a shafin Twitter na Gwamna Kaduna a ranar Laraba 7 ga watan Octoban shekara ta 2020.

Bayanin da aka wallafa a shafin ya zayyana cewa Ahmed Nuhu Bamalli shine sarki na 19 a jerin sarakuna daga masarautar ta Zazzau.

Har wayau a wata takarda da kwamishinan kananan hukumomin Ja’afaru Ibrahim Sani ya sanyawa hannu ta nuna cewa sabon sarkin Ahmed Nuhu Bamalli wanda kafin nadin sa shine Magajin Garin Zazzau ya taba kasancewa jekadan Najeriya a kasar Thailand kuma nadin say a biyo bayan rasuwar Mai Martaba Alhaji Shehu Idris ranar 20 ga watan Satunban shekara ta 2020.

Kwamishinan ya kara da cewa: “Bamalli shine sarki na farko daga tsatson Mallawa a tsawon shekaru 100 da suka gabata tun bayan rasuwar kakan sa Mai Martaba Dan Sidi a shekarar 1920”.

Kammalawa:

Rahotannin da labaran dake yawo cewa an nada Alhaji Ahmed Nuhu Bamalli a matsayin sabon sarkin Zazzau gaskiya ne.

Sanarwar nadin Bamallin ta fito ne daga kwamishina ma’aikatar kananan hukumomi ta jahar Kaduna, Ja’afaru Ibrahim Sani a wata takarda day a sanyawa hannu da kuma aka wallafa ta a shafin Twitter na gwamnan Kaduna a ranar Laraba, 7 ga watan Oktoban shekara ta 2020.

Nadin Bamallin ya biyo bayan rasuwar tsohon sarkin Zazzau Alhaji Shehu Idris a ranar 20 ga watan Satunban shekara ta 2020.

Kuna iya aikowa CDD labarai ko bayanan da kuke da shakku akansu dan ta tantance muku sahihancin su. Zaku iya turo labaran ta wannan lamba: +2349062910568 ko a shafukan mu na Twitter a @CDDWestAfrica ko @CDDWestAfrica_H

Center for Democracy and Development West Africa| CDD West Africa