Skip to main content

Gaskiyar Magana: Labari Ne Na Bogi!

Wani bidiyo mai tsawon minti hudu da dakika goma sha bakwai (4:17) da wata kafa mai suna Gido24TV dake dandalin YouTube  wanda yanzu haka ake yaduwa a WhatsApp ta wallafa ya bayyana cewa Uwargidan Shugaba Buhari, wato Aisha Buhari ta bada umarnin nan take cewa a kona ofishin shugaban ma’aikatan dake aiki a karkashin Shugaba Buhari wato Abba Kyari.

Kamar yadda wannan bidiyo da aka wallafa ranar 26 ga Maris, 2020 ya fada, umarnin ya biyo bayan gane cewa Abba Kyarin yana dauke da Cutar COVID-19 bayan da akayi masa gwaji. Bidiyon ya kara da cewa Aisha Buhari tace Abba Kyari yaje ofishin sa bayan dawowarsa daga kasar waje kuma duk abubuwan da ya bata sun harbu da Cutar COVID-19 dan haka dole a kona komai dake cikin ofis din dan akare mutane daga kamuwa da wannan cutar.

Wannan zance marar tushe har wayau kara da cewa Uwargida Aisha tace tunda kasashen duk suna ta kokarin kawar cutar kuma kawo yanzu babu maganin ta, dole ne a kona ofishin Abba Kyarin.

Binciken CCD

Masu tantance gaskiya ko rashin gaskiyar labari na Cibiyar Bunkasa Demokaradiyya Da Cigaba wato CDD sun gudanar da bincike mai zurfi kuma sun gano cewa wannan kageggen labara ne. Masu binciken sun gano cewa acikin wannan bidiyo mai tsawon minti  hudu (4) da dakika goma sha bakwai (17) babu inda aka zayyana cewa Aisha Buharin ta bada wannan umarnin ballantana rana ko lokacin da ta tayi wannan bayani.

Har wayau binciken ya gano cewa anyita anfani da hotunan Aisha Buhari da Zahra Buhari da Abba Kyari da tsohuwar ministan kudi Kemi Adeosun da hoton wuta yayin ake gabatar rahotan da ba’a ganin wanda yake gabatar dashi. Acikin wannan kageggen labari, mai gabatarwa tun da farko yayi alkawarin nunawa mai kallo yadda kona ofishin Abba Kyarin ya kasance amma har inda bidiyon ya kare ba’aga hakan ba. Kawo yanzu ankalli wannan bidiyo sau dubu shida da dari biyar kawo ranar 30th ga watan Maris, 2020 da misalin karfe 11:15 na dare, wannan yana nufin yawan masu kallon wannan labari na karya zai cigaba da karuwa.

Afili yake cewa wanda suka gina wannan labari na karya suna da aniyar samun riba ta hanyar karfafawa mutane gwiwa su cigaba da kallon wannan dandali nasu dan kuwa manhajar YouTube tana biyan kudi gare su a duk lokacin da aka kalli bidiyon, saboda haka masu kallo suna karuwa su kuma masu wannan labari na karya suna kara samun kudi.

Kammalawa:

Wannan labari, labari ne na bogi saboda haka CDD tana jan hankalin yan Najeriya da suyi watsi dashi tare da dena kallon sa dama kara yadashi a sauran kafafan sada zumunta zamani. Har wayau CDD tana kara jan hankali cewa a dena kirkira dama yada labaran karya.

Tantancewar Mu: Labari Ne Maras Tushe

#AdenaYadaLabaranKarya

Leave a Reply