Sheikh Sharif Ibrahim Saleh Bai Soki Dakatar Da Abduljabbar Nasiru Kabara Daga Wa’azi a Kano Ba!

A ranar Alhamis, 4 ga watan Maris din shekara ta 2021, masu bin diddigin labarai dan tantance sahihancin su na Cibiyar Bunkasa Demokaradiyya da Cigaba (CDD) sun gano wata murya mai tsawon minti 9 da dakika 27 da aka nada kuma ake yadawa ta manhajar WhatsApp. Acikin muryar anyi dogon sharhi tare da sukar dakatar Malam Abdujjabar Nasiru Kabara daga gabatar al’amuran wa’azi a jahar Kano sakamakon cece-kuce da maganganun sa suka janyo. Wata gabatarwa da ake yadawa da muryar tace Sheikh Shariff Ibrahim Saleh Alhussain ya yi wannan jawabi.

Acikin muryar anjiyo wani mutum na cewa: “bisa ga bayanan da muke dasu gwamnatin Kano ta rufe inda Abduljabbar ke gudanar da al’amuran wa’azi, wannan ya faru ne bayan taron dangi da malaman Darika, Sunna da sauran mazhabobi suka yi masa”

Mai sharhin ya ci gaba da cewa: “hanyar da malaman suka bi abinda dariya da kunyata kai ne, kuma dukkan mai hankali zai fahimci hakan tare da gane irin rashin adalci da aka yi masa saboda an gyara maganganu da ya yi din”

Gaskiyar Al’amura:

Binciken da CDD ta gudanar ya gano cewa muryar da ake yadawa ta manhajar WhatsApp din ba ta Sheikh Shariff Ibrahim Saleh Alhussain ba ce. Hasalima Sheikh bai yi magana akan batun dakatar Abduljabbar ba balle ya soki al’amarin.

Da CDD ta tuntubi da ga Sheikh Shariff Saleh, wato Engr. Almuntasir Ibrahim Saleh Alhaussain ya bayyana cewa muryar da ake yadawa din ba ta mahaifin sa ba ce.

Almustasir ya kara da cewa mahaifin sa bai yi tsokaci kan batun dakatar da Abduljabbar din ba,

Almuntasir y ace: “lallai na saurari muryar da ake yadawa sosai ta manhajar WhatsApp, kuma ina bada tabbacin cewa muryar ko sakon da take dauke dashi baya bayyana ra’ayin Maulana Sheikh Ibrahim Saleh Alhussain ta kowace hanya”.

Kammalawa:

Wata murya da ake yadawa ta manhajar WhatsApp inda aka jiyo wani mutum yana sukan dakatar da Abduljabbar Nasiru Kabara daga gabatar da wa’azi a jahar Kano tare da ikirarin cewa murya ce ta Sheikh Sharif Ibrahim Saleh murya ce ta bogi. Binciken CDD ya gano cewa ba muryar Shehin Malamin ba ce.

Bayanan da CDD ta tattara sakamakon bincken da ta gudanar akan batun sun nuna cewa Sheikh Sharif Ibrahim Saleh Alhsussain bai yi magana kan batun ba.

CDD na kira ga jama’a da suyi watsi da muryar tare da daina yadata.

Kuna iya aikowa CDD labaran da kuke da shakku akansu da gano muku gaskiyar su. Za ku iya turo gajeren sako (SMS) ta manhajar WhastApp akan lamba: +2349062910568 ko ku tuntube mu a shafin Twitter a @CDDWestAfrica.

#AgujiYadaLabaranBogi