Sheikh Gumi Bai Shawarci Shugaba Buhari Cewa Ya Nada Tsohon Sarkin Kano Sunusi Amatsayin Shugaban Ma’aikatan Fadarsa Ba

Tushen Magana:

A ranar Ladi, 19 ga watan Afirilun shekara ta 2020, masu tantance sahihancin labari na Cibiyar Bunkasa Demokaradiyya da Cigaba wato CDD sun gano wani labari da ake yadawa a dandalin sada zumunta na Facebook cewa sanannen malamin addinin Musuluncin nan wato Sheikh Dr. Ahmad Mahmoud Gumi ya shawarci Shugaba Muhammadu Buhari akan ya nada tsohon Sarkin Kano Muhammadu Sunusi II a matsayin shugaban ma’aikatansa fadar shugaban kasa, wato mukamin da marigayi Abba Kyari ya rike kafin rasuwarsa.

Labarin wanda aka wallafa shi da misalin karfe 12:29 na ranar Asabar, 18 ga watan Afirilun shekara ta 2020 yayi ikirarin cewa Sheikh Dr. Ahmad Gumi wanda shine babban limamin Masallacin Sultan Bello dake Kaduna ya bukaci Shugaba Buhari da ya maye gurbin marigayi Abba Kyari da tsohon Sarkin Kano, Malam Muhammadu Sunusi II.

Gaskiyar Magana:

Masu tantance sahihancin labari na Cibyar Bunkasa Demokaradiyya da Cigaba (CDD) sun tuntubi Sheikh Dr. Ahmad wanda ya nesanta kansa da wannan labarin.

Sheikh Gumi ya kara da cewa: “banyi wata magana makamanciyar wannan ba, bani da masaniya akan inda labarin ya bulla ko wadanda suka kirkire shi. Yanzu nake jin labarin daga wajenku (CDD). Batun nada shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa abune da shafi shugaban kasa kai tsaye dan haka bance komai akai ba kuma bazan ce ba, ina kira ga jama’a da suyi watsi da wannan labari na bogi”.

Kammalawa:

Sheikh Dr. Ahmad Gumi bai shawarci Shugaba Muhammadu Buhari da cewa ya nada tsohon Sarkin Kano Muhammadu Sunusi II a matsayin sabon shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa ba. Wannan labari ne na bogi saboda haka CDD na jankalin jama’a da suyi watsi dashi su kuma rika tantance kowane labari ko bayani kafin yadashi.

#AdainaYadaLabaranKarya

Leave a Comment

Your email address will not be published.