Sheikh Abdallah Gadon Kaya Baice Gwamna Zukum Ne Ya Cancanci Shugabancin Najeriya 2023 Ba!

Tushen Magana:

A ranar Talata, 23 ga watan Oktoban shekara ta 2020, masu bin diddigin sahihancin labarai na Cibiyar Bunkasa Demokaradiyya Da Cigaba (CDD) sun gano wani labari da ya mamaye zaurukan dandalin Facebook. Labarin yace sanannen malamin addinin Musluncin na dake Kano, wato Sheikh Dr. Abdallah Usman Gadon Kaya ya goyi bayan gwamnan jahar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum dan zamowa shugaban kasar Najeriya a zaben shekara ta 2023.

Labarin wanda jaridun da ake wallafawa a intanet irinsu Muryar Yanci da  Rariya da Katsina Online suka wallafa shi kuma shafin Dokin Karfe TV  ya kara yadashi, yace malamin ya suffanta Gwamna Zulum a matsayin mutumin da keda dukkanin nagartar zamowa shugaban kasa a 2023.

Kawo lokacin rubuta wannan tantancewa, mutane 5,300 ne sukace labarin ya burgesu yayin da wassu mutanen 280 suka tofa albarkacin bakin su akan labarin, karin wassu mutane 631 kuma suka kara yadashi a shafin Muryar Yanci.

Gaskiyar Magana:

Binciken da CDD ta gudanar ya gano cewa Sheikh Gadon Kaya bai goyi bayan Gwamna Zulum ko bayyana ko aiyanashi a matsayin mutumin da ya cancanci zamowa shugaban kasa a zaben shekara ta 2023 ba.

Da CDD ta tuntubeshi game dabatun, Sheikh Gadon Kaya yace ya samu labarin cewa an rawaito shi yana bayyana Gwamna Zulum a matsayin mutumin da ya kamata ya shugabanci Najeriya a zaben 2023, amma wallafa labarin aiki ne na masu son zuciya dake rubuce-rubuce a dandalin sada zumunta na zamani.

Sheikh Gadon Kaya yace: “wannan labari karya ne, ban fadi haka ba. Babu daya daga cikin kafafen da suka wallafa labarin da yayi magana dani, kirkira kawai sukayi suka wallafa labarin su”.

“ni ba dan siyasa bane kuma bana cikin wadan da keda ruwa da tsaki wajen nuna wanda zai zama shugaban kasa, ni malami ne dake fadakarwa”.

Sheikh Abdallah ya cigaba da cewa: “wadan da suka wallafa labarin sunyi anfani ne da wani wa’azi da na gabatar inda nayi magana akan yanayin da tsaro ke ciki a kasa, acikin wa’azin na yabawa Gwamna Zulum saboda jan jama’arsa ajiki tare da basu kulawa amma babu inda nace shi ya kamata a tsayar takarar shugabancin Najeriya a zaben shekara ta 2023”

Kammalawa:

Labarin da ake yadawa cewa Sheikh Dr. Abdallah Usman Gadon Kaya yace Gwamna Babagana Umara Zulum na jahar Borno ne ya kamata ya shugabanci Najeriya a shekarar 2023 karya ne, malamin bai fadi haka ba!

An jirkita jawabin da malamin ya gabatar ne lokacin da yake wa’azi kuma yayi magana akan halin da bangaren tsaro ke ciki a kasa.

CDD tana jan hankalin jama’a game da yada labaran da basu da tabbacin sahihancin su. Kuna iya aikowa CDD labaran da kuke shakku akansu dan tantance muku ta hanyar WhatsApp ko gajeren sako ta wannan lamba +2349062910568 ko a shafin Twitter a: @CDDWestAfrica ko @CDDWestAfrica_H

#AgujiYadaLabaranBogi

Center for Democracy and Development West Africa| CDD West Africa