Shan Fitsarin Rakumi da Lemon Tsami Baya Maganin Cutar Corona

Tushen Maganar: akwai wani labari na bogi da aka wallafa a shafin sada zumunta na zamani wato Facebook wanda yake ikirarin cewa shan fitsarin rakumi da lemon tsami yana maganin Cutar Corona. Wannan labari marar tushe an wallafa shi ne a ranar 30 ga watan Maris din 2020. Mawallafin ya bada tabbacin samun waraka daga Cutar Corona ga duk wanda yayi anfani da wannan labarin kanzon kurege nasa.

 Binciken Da CDD Ta Aiwatar: masu tantance labari dan gano sahihancinsa na Cibiyar Bunkasa Demokaradiyya da Cigaba wato CDD sun gano cewa wannan ikirari bashi da tushe, kuma likitoci ko masana a fannin lafiya basu bayyana hakan ba, saboda haka CDD tana jan kunne ga jama’a cewa su guji kirkira ko yada labaran karya.

Har wayau CDD tana jan hankalin mutane cewa su guji daukar duk mataki game da lafiyar su face wanda masanan lafiya suka bayar dan gudun jawowa kansu wata matsalar lafiyar.

Tantancewar Mu: Labari Ne Maras Tushe

Kammalawa:

Shan lemon tsami da fitsarin rakumi baya maganin Cutar Corona, kawo yanzu babu wani sahihin bincike daya bayyana hakan. Mutane su kiyayi baza jita-jita dangane maganin Cutar Corona. Zai fi kyau mutum yayi shiru akan abinda bashi da tabbas akai.

#AgujiYadaLabaranKarya

Leave a Comment

Your email address will not be published.