Shahararren Dan Wasan Kwaikwayo Olu Jacobs Bai Mutu Ba

Tushen Magana:

A ranar 10 ga watan Yunin shekara ta 2020 majiyoyi da yawa na yanar gizo sun bada labarin cewa shahararren dan wasan kwaikwayo nan na Nollywood mai suna Olu Jacobs ya rasu bayan gajeriayar rashin lafiya. Labaran yaja hanakalin mutane matuka gaya a dandalin Facebook da Twitter a wannan rana.

Har wayau wani shafin yanar gizo ya wallafa labarin da aka yadashi sosai a dandalin Facebook.

Gaskiya Magana:

Dan was an kwaikwayon, Olu Jacobs yananan a raye. Binciken da CDD ta gudanar ya gano cewa jita-jitar mutuwar dan was an ta samo asali ne daga shafin Nairaland ta wani labari da suka wallafa wanda suka goge daga baya.

Dan was an kwaikwayon mai shekaru 78 wanda ya taka rawa a finafinan kasar nan dama na kasashen duniya yana auren Joke Silva ne.

A lokacin da take karyata labarin, Joke tace mijinta yana nan a raye inda ta kara da cewa, “abin ya dagawa iyalan Olu Jacobs hankali wannan yasa dole muyi magana”.

Itama acikin wani martani data fitar tana karyata labarin rasuwar dan was an, kungiyar masu taka rawa a finafinai mai lakabin  Actors Guild of Nigeria (AGN) a turance, tace labarin labari ne na bogi tare da jan hankalin mutane dasu guji yada labaran karya. AGN ta bayyana dabi’ar a matsayin al’amari mai muni.

Yana labaran mutuwa game da masu taka raya a finafinai da shahararrun mutane ba sabon abu bane.

Ko a ranar 4 ga watan Yunin shekara ta 2020, said a aka yada labarin mutuwar sanannen mai taka rawa a finafinan Nollywood Hanks Anuku wanda akace ya mutu bayan gajeriyar rashin lafiya. Mai taka rawa a finafinan wanda yanzu yake rayuwa a kasar Ghana ya nadi wani hoton bidiyo inda ya karyata labarin.

Masu Taka Rawa a Finafinan Najeriya da Aka Yada Labarin Karya Game da Mutuwar Su:

A watan Yulin shekara ta 2017 an yada labarin karya day ace mai taka rawa a finafinai Ramsey Noah ya mutu, amma Ramsey ya karya wannan labari ta shafin san a Instagram a ranar 11 ga watan Yulin 2017 din.

Sanannen dan wasan kwaikwayo Chiwetalu Agu ma an yada wata jita-jita da tace ya mutu a dandalin Facebook a watan Fabrairun wannan shekara. Dan was an mai shekaru 64 yaji babu dadi game da labarin karyar inda yayi kausasan kalamai ga wadanda suka wallafa labarin karyar da yace ya mutu.

Wani wanda aka wallafa labarin karya game da mutuwarsa shine Fadeyi Oloro, dan kabilar Yoruba wanda asalin sunansa shine Ojo Arowosafe a shekara ta 2019.

Wadan su yan was an kwaikwayo da aka yada labarin karya game da mutuwarsu sune: Pete Edochie, Odunlade Adekola, Nkeam Owoh, Muna Obiekwe, Jim Iyke, Ghanian-Nigerian actor Van Vicker, Foluke Daramola, yar finafinan Hausa Maryam Yahaya wadda take taka rawa a Kannywood.

Kammalawa:

Jarumin masana’antar shirya finafinai ta Najeriya Nollywood Olu Jacobs yananan a raye. Labarin da aka yada game da mutuwar sa labari ne na bogi wanda wassu ma’abota shafukan sada zumunta da gudanar da zaurukan yanar gizo suka wallafa.

CDD tana jan hankalin mutane dasu rika tantance labari kafin yadashi saboda illolin da suke tattare dashi ga wadan da suka shafa da sauran jama’a baki daya.

Leave a Comment

Your email address will not be published.