Shafin Twitter Na Bogi Da Ke Alakanta Kansa Da Ma’aikatar Matasa Da Wasanni Ta Tarayya

Tushen Magana:

A ranar 17 ga watan Fabrairun shekara ta 2021, ayarin wasu yan kishin kasa sun janyo hankalin masu tantance sahihancin labarai da bankado labaran bogi na Cibiyar Bunkasa Demokaradiyya da Cigaba (CDD) game da wani shafin Twitter mai lakabin “Nigerian Youth Investment Fund” (NYIF_NGR) da ke ikirarin cewa shi wani tsari ne na bada tallafi ga sana’o’in matasa da gwamnatin tarayyara Najeriya ke goyon baya.

Masu lura da shafin sunyi kira ga wadan da ke bukatar tallafin fara sana’a su biya wasu kudade kafin samun tallafin.

Gaskiyar Magana:

Shafin Twitter wadda ake kira @NYIF_NGR shafi ne na bogi kuma bashi da alaka da ma’aikatar matasa da harkokin wasanni.

Binciken da CDD ta aiwatar ya gano cewa ma’aikatar matasa da bunkasa harkokin wasannin ba ta umarci masu neman kowane irin tallafi su biya kudi ba, dan haka da’awar @NYIF_NGR cewa a biya kudi karya ne.

Tsarin tallafawa matasa da jari da ma’aikatar matasa da bunkasa wasanni ta fito dashi ya kammala shirin somin-tabi a watan Yuli na shekarar da ta gabata inda mutane 239 suka amfana da N165,700,000.

Har wayau, CDD ta tuntubi mai taimakawa Ministan Matasa da Wasanni akan harkokin fasaha Areola Oluwakemi wanda ya bayyana cewa shafin Twitter din da ke neman mutane su biya kudi dan bas u tallafi shafi ne na bogi.

Oluwakemi ya kara da cewa: “wanda suka mallaki shafin kuma suke gudanar dashi na damfarar matasan Najeriya ne kawai”

Kammalawa:

Shafin Twitter wadda ake kira @NYIF_NGR shafi ne na bogi kuma bashi da alaka da ma’aikatar matasa da harkokin wasanni.

Shafin gaskiya na Twitter da ke bada bayanai game da harkokin matasa na gwamnatin tarayya shine @NYIF_NG.

CDD na jan hankalin jama’a da su tantance labarai ko sakonnin yanar gizo kafin amincewa ko aiwatar wani umarni. Mutane a kodayaushe su rika taka-tsantsan game da biya kudade ta hanyar yanar gizo musamman dan neman tallafi.

Kuna iya aikowa CDD labaran da kuke da shakku akansu dan tantance muku gaskiyar su ta hanyar aiko gajeren sako ko ta manhajar WhatsApp akan lamba: +2349062910568

#AgujiYadaLabaranBogi

Center for Democracy and Development West Africa| CDD West Africa