Sanannen Mawakin Nan DJ AB Yananan Araye!

Tushen Magana:

A ranar Ladi, 30 ga watan Agustan shekara ta 2020, masu tantance sahihancin labaria na Cibiyar Bunkasa Demokaradiyya da Cigaba (CDD) suka gano wani labari da aka yada ta dandalin Facebook dake cewa sanannen matashin mawakin nan da akafi sani da DJ AB ya rasu.

Kamar ya labarin da aka wallafa a shafin Facebook ya zayyana, mawakin ya rasu yana da shekaru 32. Wani bangare na labarin yace: “DJ AB Allah ya gafarta maka”.

Gaskiyar Magana:

Binciken da CDD ta gudanar ya gano cewa DJ AB yananan a raye kuma cikin koshin lafiya. Ba kamar ya yadda labarin da aka wallafa din ya bayyana ba, shekarun DJ AB da haifuwa 26 ne kuma an haifeshi a watan Disamban shekara ta 1993.

A martanin day a mayar game da labarin mutuwar tasa, DJ AB ya bayyana cewa labarin cewa ya mutu karya ne.

AB yace: “wannan shine karo na 85 da mutane ke rade-radin na mutum, abinda dai da ban dariya”

Kammalawa:

Sanannen matashin mawakin nan da akafi sani da suna DJ AB bai mutu ba, labarin da ake yadawa cewa ya mutu karya ne! Bayanan da muka samu daga yanar gizo akan DJ AB sun nuna cewa an haifeshi a ranar 18 ga watan Disamban 1993.

CDD tana jan hankalin jama’a da suyi watsi da wannan labari tare da tabbatar da sahihancin labari da sakonni musamman wadan da ake yadawa a yanar gizo.

Kuna aiko sako ko labarn da kuke da shakku akansu dan CDD ta tantance muku ta wannan lamba: +2349062910568.

#AgujiYadaLabaranKarya

Center for Democracy and Development West Africa| CDD West Africa

Leave a Comment

Your email address will not be published.