Salim Sani Zakariyya Ba Dan Boko Haram Bane

Tushen Magana:

A ranar Litinin, 12 ga watan Afirilun shekara ta 2021, masu tantance sahihancin labarain na Cibiyar Bunkasa Demokaradiyya da Cigaba (CDD) sun gano wani jawabi da wani mai amfani da shafin Twitter mai lakabin @UchePOkoye ya wallafa. Jawabin na dauke da hoton Salim Sani Zakariyya kuma anga wani rubutu a jikin hoton kamar haka: “Dan Boko Haram Da Ake Nema Ruwa-a-Jallo”.

Wannan jawabi da shi Uche P. Okoye ya wallafa akan Salim Sani Zakariyya na danganta shi da Boko Haram ya biyo bayan gargadi ne da Salim din ya yi masa game da yada labaran karya jim kadan bayan shi Okoyen ya ce Ministan Sadarwa Dr. Isa Ali Pantami yan cikin jerin yan ta’adda da Amurka ke nema.

Okoye ya wallafa labarin da aka yi ta yama-didi akansa da wata jaridar yanar gizo mai suna NewsWireNGR ta wallafa cewa Isa Ali Pantami na cikin yan ta’addan da kasar Amurka ke nema saboda alakar sa da wadda ya assasa kungiyar Boko Haram, marigayi Mohammed Yusuf.

Gaskiyar Al’amari:

Binciken da CDD ta gudanar ya gano cewa Salim Sani Zakariyya bashi da alaka da kungiyar Boko Haram. Binciken ya kara gano cewa Salim Sani Zakariyya baya cikin jerin wadan da Rundunar Sojin Najeriya ta wallafa a matsayin yan Boko Haram da take nema, wannan kuma kai tsaye yana karyata ikirarin da Mr. Uche yayi wa Salim din a jawabin day a wallafa a shafin sa na Twitter.

Zuzzurfan nazarin da CDD ta kara aiwatarwa ya gano cewa Mr.Okoye (@UchePOkoye) ya samu hoton Salim ne daga shafin Twitter na Salim din inda ya yi rubutu ajikin hoton day a zayyana shi Salim a matsayin dan Boko Haram da ake nema ruwa a jallo.

Da CDD ta tuntube shi, Salim Sani Zakariyya ya ce ya yi mamakin abinda Mr. Okoye ya yi masa dan kawai ya gargade shi kan yada labaran bogi.

Salim yace: “nayi mamaki yadda aka dauki hoto na kuma aka yi rubutu ajikin sa tare da bayyana ni a matsayin dan Boko Haram da ake nema ruwa a jallo, lallai wannan rashin adalci ne karara kuma abin takaici, abinda ya janyo haka shine gargadin da na yiwa shi Mr. Okoye game da yada labarin da bashi da tabbacin sa”

“Ganin cewa labarin da ya wallafa labari ne na bogi sai nayi tsokaci inda naja hankalin sa game da hakan amma kawai sai ya dauki hoto na rubuta cewa ni dan Boko Haram ne kuma ya yada a shafin sa”.

Kammalawa:

Wani hoto da ake yadawa a shafukan sada zumunta na zamani da ke bayyana Salim Sani Zakaraiyya a matsayin dan Boko Haram da ake nema ruwa a jallo hoto ne na bogi.

Wanda ke cikin hoton, Salim Sani Zakariyya ba dan Boko Haram bane, hoton sa kawai aka dauka a shafin Twitter akayi rubutu bayan ya janyo hankalin wani mai amfani da shafin “Uche P. Okoye (@UchePOkoye) game da yada labaran bogi.

CDD na jan hankalin jama’a kan tantance sahihancin labari kafin yada shi ga sauran mutane.

Kuna iya aikowa CDD labaran da kuke da shakku akan su dan tantance muku gaskiyar su ta hanyar aiko gajeren sako SMS ko ta manhajar WhatsApp akan lamba +2349062910568 ko a shafin Twitter ta wannan adireshi: @CDDWestAfrica

#AgujiYadaLabaranBogi

Center for Democracy and Development West Africa| CDD West Africa