Rundunar Tsaro Ta SSS Bata Kama Masu Zanga-Zanga a Kano Ba

Tushen Magana:

A ranar Asabat, 17 ga watan Oktoban shekara ta 2020, masu tantance sahihancin labarai na Cibiyar Bunkasa Demokaradiyya (CDD) suka gano wani labarai da jaridu da wassu majiyoyi suka wallafa dake cewa hukumar tsaron farin kaya ta State Security Service (SSS) sun kama mutane da sukayi zanga-zangar neman kawo karshen halin rashin tsaro da yankin arewacin Najeriya, acewar labarin ankama masu zanga-zangar ne a birnin Kano.

Labarin wanda jaridun Punch da the Cable da Inside Arewa News suka rawaitowo ya bayyana cewa jami’a tsaron farin kaya na SSS sun garkame jagororin zanga-zangar neman kawo karshen sata da garkuwa da mutane dan neman kudin fansa da tashe-tashen hankula a yankunan karkara da sauran tashe-tashen hankula dake da nasaba da rashin tsaro a yankin arewacin Najeriya.

Labarin ya kara da cewa SSS ta kama su ne a Kano.

Gaskiyar Magana:

Binciken da CDD ta gudanar ya gano cewa hukumar tsaron farin kaya ta SSS bata kama kowa ba acikin wadan da sukayi zanga-zanga a jahar Kano.

Binciken ya gano cewa SSS ta gayyaci jagororin gamayyar kungiyoyin arewa karkashin shugabancin Nastura Ashir Sharif. Gayyatar jagororin ya biyo bayan zanga-zangar da suka shirya gudanarwa ne dan nuna rashin jin dadin su game da halin rashin tsaro da yankin arewa yake ciki tare da neman gwamnati kalli lamarin dan samar da tsaro.

Shugabannin zanga-zangar sun isa ofishin SSS ranar Juma’a, 16 ga watan Oktoban shekara ta 2020 da misalin karfe 9:30 na dare kuma ganawar su da jami’an tsaron farin kayan ta dauki sama da awa shida (6).

Washe gari Asabat, 17 ga watan Oktoban shekara ta 2020, masu zanga-zangar sun gabatar da zanga-zangar tasu inda suka fara daga Daula Hotel zuwa matsugunin hukumar yan sanda reshen jahar Kano dake Bompai, Kano.

Masu zanga-zangar sun mika takardar korafi ga kwamishinan yan sanda jahar Kano.

Da yake maida martani game da kama sun, shugaban gamayyar kungiyoyin arewa, Nastura Ashir Sharif yace SSS bata kama ko daya daga cikin masu zanga-zangar ba.

Yace yace: “abinda ya faru shine, ranar Alhamis, 14 ga watan Okotban shekara ta 2020 mun shirya yin zanga-zanga amma da farawar mu sai aka turo yan daba sukazo suka wargaza mutane da makamai inda suka jikkata mutane da yawa acikin su har da yan jaridu guda hudu. Saboda haka ranar washe garin Juma’a sai muka kira taron manema labarai inda mukayi Allah-wadai da abinda ya faru dan lokacin da aka mana harin yan sanda suna nan amma suna ganin yan daban suka jikkata mutane ba tare da yin komai ba”.

“Mun shirya cigaba da yin zanga-zangar ranar Asabat 16 ga watan Oktoban shekara ta 2020 amma sai yan sanda da SSS sukace ba za’a gdanar da zanga-zangar ba, wannan yasa suka gayyace mu. Mun tambaye su ko menene dalilin da yasa ba za’a gudanar da zanga-zanga a Kano ba, mun gaya musu cewa zanga-zanga yancin mu ne a matsayin mu na yan kasa. Ana zanga-zanga a kudancin kasarnan, me yasa kuke so ku dakatar damu daga yin zanga-zangar lumana? Munyi tattaunawa mai tsawon gaske dasu kafin mu cimma matsaya”.

“Dalilan da suka sa mutane ne ke rade-radin cewa ankama mu shine mun dauki tsawon lokaci a ofishin SSS din kuma sauran mambobi suna ta kiran wayoyin mu ba’a dauka dan haka sai suke tunanin an kama mu ne. Tun karfe 9:30 na dare muke ofis din SSS din kuma har karfe 3 na dare muna can, wannan yasa akayi tunanin an kama mu ne, amma ba kama mu akayi ba”.

Kammalawa:

Labarin da ake yadawa cewa hukumar tsaron farin kaya ta SSS ta kama masu zanga-zanga a Kano karya ne.

Binciken da CDD ta gudanar ya gano gamayyar kungiyoyin arewa sun fara zanga-zangar neman kawo karshen rashin tsaro a arewacin Najeriya ranar Alhamis, 15 ga watan Oktoban shekara ta 2020 da nufin cigaba da zanga-zangar ranar Asabat, 17 ga watan Oktoba amma sai rundunar tsaro ta SSS ta gayyace su ranar Juma’a 16 ga watan Oktoba.

Bayan barin ofishin SSS din dake Kano da tsakiyar daren Juma’a, jagororin zanga-zangar sun aiwatar da zanga-zangar ranar Asabat, 17 ga watan Oktoba, 2020.


Kuna iya aikowa CDD labarai ko bayanan da kuke da shakku akansu dan ta tantance muku sahihancin su. Zaku iya turo labaran ta wannan lamba: +2349062910568 ko a shafukan mu na Twitter a @CDDWestAfrica ko @CDDWestAfrica_H

Center for Democracy and Development West Africa| CDD West Africa