Raymond Abbas Da Akafi Sani Da Suna Hushpuppi Yana Cigaba da Zama a Gidan Yari a Kasar Amurka

Tushen Magana:

A ranar Laraba, 22 ga watan Yulin shekara ta 2020, masu tantance sahihancin labari na Cibiyar Bunkasa Demokaradiyya da Cigaba (CDD) suka gano wani labari da akayita yadawa shafukan sada zumunta na zamani cewa ansaki Raymond Abbas da akafi sani da suna Hushpuppi daga gidan yari a kasar Amurka inda ake rike dashi dan jiran shari’a bisa zargin aikata zanba cikin aminci da danfara.

Labarin wanda aka yadashi sosai a dandanlin WhatsApp da sauran shafukan sada zumunta na zamani ya bayyana cewa Hushpuppi ya shaki iskar yanci daga zarge-zargen da ake masa na aikata danfara ta hanyar yanar gizo.

Zaurukan yanar gizo da yawa sun wallafa labarin, GH Gossip na daya daga cikin su

Binciken da masu tantance sahihancin labarai na CDD sun gano cewa labarin cewa ansaki Hushpuppi karya ne.

Abinda ya faru shine, Hushpuppi wanda ake zargi da aikata danfara, an canja inda ake tsare dashi ne. Hukumar binciken manyan laifuka ta kasar Amurka FBI ta sauya masa matsuguni ne daga wani gidan yari zuwa wani.

Hoton Hushpuppi da za’a iya gani daga sama acikin wannan jawabi hoto ne da aka samo shi daga shafin yanar gizo na hukumar binciken manyan laifuka ta kasar Amurka FBI an wallafa shi ne a ranar 20 ga Yulin shekara ta 2020.

Da yake jawabi dangane da batun, lauyan Hushpuppi, Gal Pissetzky ya bayyana cewa an canzawa wanda yake karewa wato Hushpuppi gidan yari ne daga inda aka fara tsare shi dan fara fuskantar shari’a.

Jaridar  Premium Times ta rawaito lauyan Hushpuppi yana cewa “ba gaskiya bane cewa ansaki Hushpuppi, kawai an canja masa gidan yari ne inda aka mayar dashi jahar California”.

A ranar Laraba, 22 ga watan Yulin shekara ta 2020, lauyan ya gayawa manema labarai cewa canjawa Hushpuppi gidan yari baya nufin sake shi.

Idan za’ iya tunawa dai a farko watan Yulin da muke ciki ne yan sanda a hadaddiyar daular larabawa ta Dubai suka café Hushpuppi bias zargin danfarar mutane ta hanyar yanar gizo daga sassa daban-daban na duniya kudade da yawan su yakai 1,926,400. Zargin dake kansa shi kadai na danfarar mutane yakai kudade da yawansu yakai biliyan 168. Anfara gabatar dashi a wata kotu da take Chicago kafin daga baya a mayar dashi California.

A halin yanzu hukumar binciken manyan laifuka ta kasara Amurka wato FBI ne ke lura da shari’ar Hushpuppi din.

Kammalawa:

Labarin da ake yadawa cewa ansaki Hushpuppi karya ne. Kawai an canjawa Hushpuppi gidan yari ne inda aka mayar dashi wani gidan yari a California inda zai cigaba da fuskantan shari’a akan zarge-zargen da suka shafi danfara.

CDD na jan hankalin jama’a das u guji yada labaran da basu da sahihanci, CDD har wayau na karfafawa mutane gwiwa da su rika tantance sahihancin labarai kafin yada su.

Kuna iya aikowa CDD labaran da kuke da tantama akansu domin tantancewa ta wannan lambar waya: +2349062910568 ko a shafin Twitter ta hanyar wannan adireshi: @CDDWestAfrica @CDDWestAfrica_H.

##AgujiYadaLabaranBogi

Leave a Comment

Your email address will not be published.