NCDC Bata Zargi Matasan Najeriya da Yada Cutar Corona a Najeriya Ba

Tushen Magana:

A ranar 3 ga watan Yulin shekara ta 2020, mafiya yawan kafafen yada labarai sun wallafa wani labari inda suka ce babban daraktan hukumar dakile yaduwar cututtuka ta kasa NCDC, Dr. Chikwe Ihekweazu ya zargi matasan Najeriya da yada cutar Corona a fadin Najeriya baki daya. Kafafen yada labaran da suka wallafa wannan labari sun hada da jaridar The Nation, Linda Ikeji blog, PMNews and Punch.

Labarin yace babban daraktan NCDC din yayi zargin ne yayin da yake tsokaci a lokacin da kwamitin shugaban kasa akan wannan annoba ta cutar Corona ke yiwa yan manema labarai a Abuja.

Kamar yadda labarin ya zayyana, Dr. Chikwe yace matasan Najeriya sune keda alhakin yada cutar Corona a kasar.

Kamar yadda shafin yanar gizo na jaridar Punch wadda itace kafa ta farko da ta wallafa wannan labari, yace: “NCDC ta zargi matasan Najeriya da yada cutar Corona”.

Gaskiyar Magana:

Binciken da CDD ta gudanar ya gano cewa babban daraktan hukumar NCDC din bai zargi matasan Najeriya da yada cutar Corona ba.

Nazari mai zurfi da CDD ta gudanar akan jawabin da babban daraktan hukumar NCDC ya gabatar ya nuna cewa daraktan yana janyo hankali ne game da bayanan da hukumar take dashi day a nuna cewa yan dake tsakanin shekaru 20 zuwa 40 sune wannan cutar tafi kamawa.

Wani sashi na jawabin babban daraktan hukumar NCDC din “yayin da cutar Corona ke cigaba da yaduwa a duniya, kamar yadda kuke ganin alkaluman, yaduwar cutar Corona yafi yawa a tsakanin matasa, amma ba yara ba, mutane dake tsakanin shekaru 20 zuwa 40 kamar yadda bayanna  mu suka nuna, mutane dake tsakin wadannan shekaru suke kan gaba wajen yada wannan cuta kodayake wadan da ke jin radadin wanann cuta sune mutanen dake sama da shekaru 50”.

Chikew ya kara da cewa: “3 daga cikin mutane 5 da cutar Corona ta hallaka mutane ne yan sama da shekaru 50, wannan yana nufin sai mun sake zage damtse wajen aiki tukuru dan dakile cutar. Dukkanin mu dole muyi aiki sosai wajen kare wadanda suke suka cim musu. Muna daf da bude filaeyn tashi da saukar jiragen saman mu, tuni an sassauta tafiye-tafiye ta jirgi tsakanin jihohi”.

A wani sakon da ya wallafa a shafin san a Twitter, Dr. Chikwe yace: “acikin jawabi na, na jaddada cewa daga bayanan da muke dasu mafiya yawa daga cikin masu dauke da cutar Corona suna tsakanin shekaru 20 da kuma 40 yayind wadanda suka fi mutuwa suka kasance masu shekaru 50 zuwa sama. Bama zargin kowane rukuni na mutane da yada cutar saboda kowane rukunin al’umma yana da muhimmanci a garemu. Dole mu jajirce dank are kowa da kowa musamman tsofi da kuma masu rauni acikin al’umma”.

Yana da muhimmanci mu sani cewa matasa sune mafiya yawa a Najeriya kuma yawansu ya zarce kaso 60 na yawan yan Najeriya.

A wani gyara cikin gaggawa da ta gudanar game da labarin da ta wallafa, jaridar Punch ta sauya jigon labarin da ta buga tun farko, jigon labarin da ta buga da farko shine: “NCDC ta zargi matasan Najeriya da yada cutar Corona”, yanzu kuma jaridar ta kwaskware wannan jigon labari inda ya koma: “cutar Corona tana yaduwa kamar wutar daji a tsakanin matasa-a cewar NCDC”.

Kawo karfe 8 na safiyar ranar 3 ga watan Yulin shekara ta 2020, mutane 27,110 ne suka kamu da cutar Corona yayin da mutum 10,801 suka warke kuma aka sallame su, wassu mutanen 616 sun mutum sakamakon kamuwa da wannan cuta.

Kammalawa:

Babban daraktan hukumar dakile yaduwar cututtuka ta kasa NCDC bai zargi matasan Najeriya da yada cutar Corona ba. Babban daraktan, Dr. Chikwe Ihekweazu yayi anfani da bayanan da hukumar sa take dashi ne inda yace daga cikin mutanen dake dauke da cutar matasa sunfi yawa.

Ihekweazu ya kara da cewa tsofi sunfi fuskantar barazanar mutuwa daga cutar saboda haka ya shawarci dukkan yan Najeriya da suyi mai yiwuwa dan kare tsofi dama mutane masu rauni daga cikin al’umma.

CDD tana jan hankalin mutane da su rika tantance sahihancin labarai kafin yada su.

#AdainaYadaLabaranKarya

Summary

Tantancewar Da CDD Ta Aiwatar

NCDC Bata Zargi Matasan Najeriya da Yada Cutar Corona a Najeriya Ba

Babban daraktan hukumar dakile yaduwar cututtuka ta kasa NCDC bai zargi matasan Najeriya da yada cutar Corona ba. Babban daraktan, Dr. Chikwe Ihekweazu yayi anfani da bayanan da hukumar sa take dashi ne inda yace daga cikin mutanen dake dauke da cutar matasa sunfi yawa.

Ihekweazu ya kara da cewa tsofi sunfi fuskantar barazanar mutuwa daga cutar saboda haka ya shawarci dukkan yan Najeriya da suyi mai yiwuwa dan kare tsofi dama mutane masu rauni daga cikin al’umma.

CDD tana jan hankalin mutane da su rika tantance sahihancin labarai kafin yada su.

#AdainaYadaLabaranKarya

Leave a Comment

Your email address will not be published.