Minista Sadiya Farouk Bata Ce Yan Arewacin Najeriya Masu Karamin Karfi Ne Kawai Zasu Samu Tallafin Gemanitin Tarayya Ba

Jita-Jitar Da Ake Yadawa:

Wani sako da ake yadawa ta shafin Instagram yace Ministan Bada Dauki da Jinkai Sadiya Farouk tace masu karamin karfi yan arewa ne kawai suka cancanta su samu tallafin gwamnatin tarayya ta hanyar banki da za’a raba a wannan lokaci da ake kokarin yakar Cutar Corona. Labarin bogin da aka wallafa yana dauke da hoton ministan kuma angina labarin da jigo kamar haka “zamu raba tallafin kudi na gwmnatin tarayya ga yan arewa talakawa ne kawai saboda babu talakawa a kudancin Najeriya”.

Gaskiyar Magana:

Wannan labari da ka’iya tunzura mutane kuma marar tushe bashi da madogara. Idan za’a iya tunawa, ministan tayi jawabi a ranar Litinin da Talata wato 30 da 31 ga watan Maris, 2020 a lokacin da take tare da sauran mambobin kwamitin gwamnatin tarayya akan Cutar Corona, a lokacin jawabin, Sadiya Farouk tace yan Najeriya masu rauni dake jihohi 36 da babban birnin tarayya Abuja sune zasu samu tallafin gwamnatin tarayya ta hanya tura musu kudi ta banki.

Tallafin gwamnatin tarayyar zai shafi iyalai masu karamin karfin ne a duk fadin Najeriya ba tare da bada kulawa ko fifiko ga wani yanki ba. An samar da wani jadawali da za’a samar dashi a dukkan jihohi dan tattara bayanan wanda suka cancanta su samu tallafin, kuma da wannan jadawali ne za’ayi anfani wajen aiwatar tsarin tallafin.

Kammalawa:

Jita-jitar da ake yadawa cewa gwmantin tarayya zata raba kudi ga yan arewancin Najeriya dan rage musu radadin rayuwa musamman a wannan lokaci da ake yakar Cutar Corona labari ne na bogi. Cibiyar Bunkasa Demokaradiyya da Cigaba wato (CDD) tana jan hankali ga yan Najeriya da suyi watsi da wannan labari da ka’iya tunzura mutane da kuma kira da adaina kirkira ko yada labaran karya.

Leave a Comment

Your email address will not be published.