Minista Sadarwa Bai Ce Rashin Yin Rijistar NIN Zai Janyo Daurin Shekaru 14 a Gidan Yari Ga Mutane Ba

Tushen Magana:

A ranar Juma’a, 2 ga watan Afirilun shekara ta 2021, masu bin diddigin labarai da gano sahihancin su na Cibiyar Bunkasa Demokaradiyya da Cigaba (CDD) sun gano wani labari da tarin masu amfani da kafafen sada zumunta na zamani suka wallafa. Labarin ya ce Ministan Sadarwa Dr. Isa Ali Ibrahim Pantami ya gargadi jama’a game da fuskantan hukuncin daurin shekaru 14 a gidan yari idan suka gaza yin rijistar NIN.

Kamar yadda labarin ya zayyana, Pantami ya furta hakan ne lokacin da yake jawabi a wani taron manema labarai da sashin yada labarai na fadar shugaban kasa ya shirya ranar Alhamis din da ta gabata.

Gaskiyar Al’amari:

Nazari da binciken da CDD ta gudanar game da labarin da ake yadawa cewa Ministan Sadarwa yace duk wadda baiyi rijistar NIN ba zai fuskanci zama a gidan yari na tsawon shekaru 14 ya gano an jirkita labarin.

CDD har wayau ta gano cewa Pantami ya ce mafiya yawan yan Najeriya basu mallaki lambar NIN ba said a batun rufe layukan waya ya taso.

A jawabin da Pantami ya gudanar a taron manema labarai da CDD ta samu kwafin sa daga shafin YouTube na Channels TV, Pantamin ya ce: “mallakar shedar dan kasa doka ce kuma dole akan kowa”.

Da yake kara bayani kan dokar da kuma yawan shekarun ta, Pantami ya ce aiwatar da wasu al’amura ba tare da mallakar lambar NIN ba saba doka ne.

Pantami ya ciga ba da cewa: “laifi ne mutum ya mallaki katin zabe idan bashi da lambar NIN bisa hurumin sashi na 27 na dokar NIMC. Laifi ne mutum ya bude asusun ajiya a banki ba tare da lambar NIN ba.

“Haka nan biyan haraji ba tare da wannan lamba ba laifi ne, laifi ne ma mutum ya karbi pancho ba tare da mallakar NIN ba. Cin gajiyar gwamnati ta kowace hanya ba tare da mallakar NIN ba laifi ne. Sashi na 29 ya ce duk wanda yayi da daga cikin wadannan al’amura da  sashi na 27 yayi magana akan su ba tare da mallakar katin shedar dan kasa na ba ya aikata laifin da ka iya janyo masa cin tara ko zama a gidan yari ko ma duk hukunci guda biyun, wannan hukunci kuma tsawon shekaru 14 ne”, inji Pantami.

Karin binciken CDD ya gano cewa wannan doka da Pantami yayi magana akanta an samar da ita ne tun shekara ta 2007 lokacin da aka kirkiri hukumar katin dan kasa NIMC. Bayan cece-kucen da maganar tasa ta janyo, Pantami yayi magana ta shafin sa na Twitter inda ya bukaci yan jarida da su fitar muryar sa suka nada tare da bayyana cewa basu rawaito abinda ya fada daidai ba.

Kammalawa:

Labarin da ake yadawa cewa Ministan Sadarwa Dr. Isa Ali Pantami ya gargadi yan kasa kan mallakar lambar NIN ko su fuskanci zama a gidan yari na tsawon shekaru 14 na cike da rudani kuma an jirkita shi.

Nazarin da CDD ta gudanar ya gano cewa Ministan yayi magana ne akan abinda hurumin doka ya fada game da lambar dan kasa da kuma tsawon shekarun da dokar ta kwashe tun bayan samar da ita.

CDD na jan hankalin jama’a kan tantance sahihancin labari kafin yada shi ga sauran mutane.

Kuna iya aikowa CDD labaran da kuke da shakku akan su dan tantance muku gaskiyar su ta hanyar aiko gajeren sako SMS ko ta manhajar WhatsApp akan lamba +2349062910568 ko a shafin Twitter ta wannan adireshi: @CDDWestAfrica

#AgujiYadaLabaranBogi

Center for Democracy and Development West Africa| CDD West Africa