Mataimakin Kwamishinan Yan Sanda Da Matsafa Suka Harba Yana Nan Araye!

Tushen Magana:

A ranar Asabat, 14 ga watan Nuwanban shekara ta 2020 jaridar The Nation ta wallafa wani labari inda tace mataimakin kwamishan yan sanda a jahar Edo ya rasu sakamakon harbin sad a matsafa sukayi yayin da yake musayar wuta da matsafan.

Labarin yace, mataimakin kwamishinan yan sandan wanda shine ke lura da rundunar yan sandan dake birnin Benin ya rasu ne ranar Juma’a, 13 ga watan Nuwanba, 2020 a asibitin koyarwa na Jami’ar Benin.

Labarin ya kara da cewa an samu bayanin mutuwar mataimakin kwamishinan yan sandan ne ta hanyar wani babban jami’in yan sandawadda yayi magana ta hanyar waya.

Gaskiyar Magana:

Binciken da CDD ta gudanar ya gano cewa mataimakin kwamishinan yan sanda mai suna ACP Agabi Godiri yana nan a raye.

CDD har wayau ta gano cewa an jikkata ACP Godiri yayin day a fafata da matsafa a titin Upper Sakponba dake wajen birnin Benin amma yana cigaba da samun kulawa a asibiti, dan jarida mai kawo labarai daga bangaren tashe-tashen hankali Festus Alenkhe ya tabbatar da hakan.

Alenkhe ya kara da cewa: “mataimakin kwamishinan ya sandan baya sanye da kaki kuma yana tuki ne sai kawai ya tsinci kansa a inda harbe-harben ke faruwa, yadan samu raunuka amma sai yayi maza-maza ya tuka motar sa yabar wajen inda ya bukaci dauki dan kaishi asibiti kuma yanzu haka yana samun kulawa”

Za’a sallami Godiri daga asibiti nan bada dadewa ba, inji Alenkhe.

CDD ta samu hoton dake nuna ACP Godiri anyi masa aiki a kafadar sa yayin da wani abokin sa ke zaune a gefen sa a asibiti a birnin Benin.

Wassu majiyoyi da suka hada da Premium Times sun rawaito kwamishinan yan sanda Johnson Kokumo yana cewa Godiri da sauran yan sanda da suka samu raunuka suna samun sauki a asibiti.

Kammalawa:

Labarin da ake yadawa cewa mataimakin kwamishinan yan sanda ACP Agabi Godiri ya mutu bayan da matsafa suka bude masa wuta a birnin Benin karya ne. Godiri yana nan araye yana cigaba da samun sauki a asibiti.

CDD tana jan hankalin jama’a game da yada labaran da basu da tabbacin sahihancin su. Kuna iya aikowa CDD labaran da kuke shakku akansu dan tantance muku ta hanyar WhatsApp ko gajeren sako ta wannan lamba +2349062910568 ko a shafin Twitter a: @CDDWestAfrica ko @CDDWestAfrica_H

Center for Democracy and Development West Africa| CDD West Africa