Lakabin Black Friday Baya Nufin Muzantawa Ga Ranar Juma’a

Tushen Magana:

A ranar Alhamis, 27 ga watan Nuwanban shekara ta 2020 masu bin diddigin labarai dan gano sahihancin labarai na Cibiyar Bunkasa Demokaradiyya da Cigaba (CDD) sun gano wata takarda data fito daga hukumar HISBA ta jahar Kano, takardar wadda aka aikata ga hukumar gudanarwar gidan rediyon Cool FM dake birnin Kano ta nemi da a dakatar da tallace-tallacen da ake sakawa a rediyon da suka danganci ranar da aka yimata lakabi da “Black Friday”, ma’ana bakar Juma’a. Lakabin “Black Friday” bai dace ba a cewar hukumar HISBA kuma muzanta ranar Juma’a ne a matsayin tat a ranar mafi daukaka a jerin raneku.

Wani bangare na takardar yace: “muna san mun bayyana rashin jin dadin mu bisa abinda aka yiwa lakabi da “Black Friday”, hakanan muna janyo hankali da cewa mafiya yawa na al’ummar jahar Kano Musulmai ne kuma sun dauki Juma’a a matsayin rana madaukakiya, dan haka hukumar gudanarwar wannan gidan rediyo ta daina kiran Juma’a a matsayin “Black Juma’a” ba tare da bata lokaci ba.

Gaskiyar Magana:

CDD ta tuntubi Kwamandan Hukumar HISBA ta jahar Kano, Sheikh Haroun Muhammad Ibn Sina wanda ya tabbatar da cewa takardar da ingancin takardar da kuma fitowa daga hukumar sa tare da aikata ga manajan Cool FM Kano.

CDD har wayau ta samu samu bidiyo da sautin murya da aka nada inda Kwamandan HISBA din yayi dogon bayani akan abinda “Bakar Juma’a” ke nufi.

Ta cikin wata tattaunawar da CDD tayi da Kwamandan hukumar HISBA, Sheikh Ibn Sina, yace kodayake basa goyon bayan suffanta ranar Juma’a a matsayin “Bakar Juma’a”, basu dakatar kowane rediyo daga kiran wannan rana ba.

Ibn Sina ya kara da cewa: “Juma’a ran ace mai muhimmanci kuma itace rana da tafi albarka daga cikin jerin raneku, muna ganin bai dace a suffanta ta da “Bakar Juma’a” ba, abinda muakyi shine fadakar da Musulmai akan haka”

“Munja hankalin Musulmai akan haka tare da girke dakarun mu a duk wuraren taruwar jama’a da kasuwanni dan dakatar da cudanya tsakanin maza da mata dama tabbatar da cewa mutane basuyi shigar da ta sabawa addini ba. Mu hukuma ce da jaddada halayyar kwarai da kuma dakatar da abinda ya sabawa addinin Musulunci”

Ibn Sina ya kara da cewa: “bamu dakatar kowa daga aiwatar da wassu al’amura a wannan rana ba”

Kwamandan HISBAn ya kara da cewa basu dakatar da komai daga faruwa ba a wannan rana, kawai abinda suke kyama shine aiyana ranar ta Juma’a a matsayin “Baka” da cudanyar matasa maza da mata da zai janyo suki halartar Sallar Juma’a, wannan kuma abune da hukamar take kokarin hana faruwar sa.

Binciken da CDD ta gudanar ya gano cewa “Black Friday” kamar yadda ake kiran ta ta samo asali ne daga kasar Amurka kuma wani suna ne da aka samar dashi ake kuma yin kwarya-kwarya tunawa dashi tun shekarar 1952.

Tarihi ya nuna cewa anfara tunawa da wannan rana shekarar 1950 kuma kuam yan sanda a garin Philadelphia sun baiwa ranar sunan ne dan siffanta wani rikici da ya faru lokacin da wassu ayarin masu sayayya da masu yawon bude ido suka cika birnin kafin gudanar wani kwallo da sojoin ruwa ke gudanarwa da kuma akeyi a wata ranar ta kowace shekara. Sakamakon cikar kwari da garin na Philadelphia yayi aiki yayi yawa ga yan sandan saboda kula da sufuri acikin birnin, kuma wannan al’amari ya samar da damuwa ga yan sandan.

A baya-bayannan kasashe da yawa ciki hard a Najeriya sun maida wannan rana ta zama wata rana da masu saida kayayyaki ke saida ababen sayarwa cikin farashi mai rahusa, hakanan masu sayan kayyaki na tattali dan jiran wannan rana dan sayan kayayyaki cikin farashi mai sauki.

Bugu-da-kari lakabin “Black Friday” bashi da wata illa, kuma bakaken mutane sunyi yawa a duniya, hakanan Najeriya da daga cikin kasashen bakaken fata a nahiyar Afrika, kuma yan Najeriya bakake ne.

Kammalawa:

Lakabin “Black Friday” lakabi ne da ake anfani dashi wajen sayar da kayayyaki cikin farashi mai sauki kuma ranar ta samo asali ne daga kasar Amurka hakanan, tunawa da ranar ya karade duniya.

CDD tana jan hankalin jama’a game da yada labaran da basu da tabbacin sahihancin su. Kuna iya aikowa CDD labaran da kuke shakku akansu dan tantance muku ta hanyar WhatsApp ko gajeren sako ta wannan lamba +2349062910568 ko a shafin Twitter a: @CDDWestAfrica ko @CDDWestAfrica_H

#AgujiYadaLabaranBogi

Center for Democracy and Development West Africa| CDD West Africa