Labarin da aka Wallafa Cewa Shugaba Buhari Yayiwa Tsohuwa Yar Shekaru 70 Fyade A Shekarun Baya Karya Ne!

Tushen Magana:

A ranar Labara, 3 ga watan Yunin shekara ta 2020, masu tantance sahihancin labarai na Cibiyar Bunkasa Demokaradiyya da Cigaba sun gano wani labari da wassu shafukan yanar gizo guda biyu suka wallafa cewa wata tsohuwa yar shekara 70 tana zargin cewa Shugaba Muhammadu Buhari dayi mata fyade a shekarun baya.

Kamar yadda labarin ya zayyana, Shugaba Buhari ya aikata lamarin ne a shaekara 1972.

Ga yadda aka gina jigon labarin: “acikin hoto mai motsi (bidiyo) wata tsohuwa tayi zargin cewa Shsugaba Buhari yayi mata fyade a shekarar 1972, wannan bidiyo yana shan kallo, gama hotuna dan Karin bayani”

Jim kadan da wallafa wannan labari, mutane sama da dubu daya ne suka karanta shi yayi wassu mutane 800 sukayi mu’amila dashi kawo lokacin hada wannan tantancewa.

Gaskiyar Magana:

Bayan da masu tantance sahihancin labari na CDD suka gano jan hankalin da labari yake yi sun gudanar da bincike game da inda labarin ya samo asali sai suka gano cewa wassu zauran yanar gizo da suka yi suna wajen kirkira da yada labaran karya ne suka wallafa shi. Zaurukan sune: Cyoungblogs da Legitfund. 

Ko a watan Afirilun day a gabata saida daya daga cikin zaurukan ya wallafa wani labarin bogi inda yace: “Na rabawa dukkan yan Najeriya  naira dubu 5000 ta hanyar anfani da kariyar su ta BVN-inji Tsohon Shugaban Kasa Obasanjo. Bayan wallafa wannan labari CDD ta aiwatar da bincike inda ta gano cewa labari ne na bogi kuma ta wayar da kan jama’a game dashi.

Binciken CDD ya gano cewa Cyoungblogs suna wallafa labari ne a wani kanfani mai suna Golden Media Nigeria wanda ke mabiya dubu dari takwas (800,000) a dandalin Facebook kuma sunyi suna wajen wallafa labaran karya dama jirkitattun labarai.

Kodayake jigon labarin yayi alkawashin nuna bidiyon da tsohuwar tayi wannan zargi da bakinta amma ba’ayi hakan ba, wannan ma wata alama ce dake nuna cewa labari ne na karya kuma angina shi ne dan jan hankalin mutane.

Har wayau hotunan da labarin yayi alkawarin nunawa masu karanta labarin ba’a nuna su ba, hasalima idan mutum ya latsa inda ya kamata ya kalli hoto sai akaishi wajenda inda zai kalli tallace-tallace.

A lokacin da CDD ta tuntube shi game da batun, mai taimakawa Shugaba Muhammadu Buhari ta bangaren kafafen sada zumunta na zamani, Bashir Ahmad ya bayyana labarin a matsayin labarin bogi kuma marar tushe balle makama.

Ahmad ya kara da cewa: “zargin zargi ne maras tushe hakanan labarin bogi, kuma bangaren kafafen sada zumunta na zamani yana sane da labarin kuma tuni ya mikashi hukumomin da suka kamata dan daukar matakin da ya dace”

Kammalawa:

Babu wata tsohuwa yar shekara 70 da ta zargi Shugaba Muhammadu Buhari da yimata fyade acikin bidiyo. Wassu shafukan yanar gizo da sukayi suna wajen kirkira da yada labaran bogi ne suka kirkiri labarin, dan haka CDD tana kira ga mutane da suyi watsi da labarin tare da daina yadashi.

Leave a Comment

Your email address will not be published.