Labaran Karya da CDD ta Gano Tare da Binciko Sahihancin Su a Mako na Uku na Watan Maris, 2021

A mako na uku na watan Maris din shekara ta 2021, masu bin diddigin labarai dan gano sahihancin su na Cibiyar Bunkasa Demokaradiyya da Cigaba (CDD) sun bankado tare da binciko gaskiyar wasu labaran karya da aka wallafa a kafafen sada zumunta na zamani irin su Facebook, Twitter da manhajar WhatsApp. Ga labaran nan kamar yadda wannan mujalla ta mu ta wallafa su:

Shin Gwamnatin Tarayya Na Bada Tallafin N30,000 a Zango Na Biyu Na Bullar Cutar Korona?

Masu tantance sahihancin labarai dan gano sahihancin sun a Cibiyar Bunkasa Demokaradiyya da Cigaba (CDD) sun gano wani labari da ake yadawa ta manhajar WhatsApp. Labarin na cewa yanzu haka gwamnatin tarayya na bada tallafin N30,000 ga jama’a a matsayin tallafi rage radadin da cutar Korona ta haifar a wannan zagaye na biyu da cutar ke kunno kai. A cewar labarin, za a rika baiwa yan Najeriya naira dubu talatin kowane sati dan cigaba da rayuwa acikin wannan zango na biyu na cutar ta Korona.

Binciken da masu bin diddigin labarai dan gano sahihancin su na CDD suka gudanar ya gano cewa ikirarin da labarin yayi cewa gwamnatin tarayya na bada tallafin naira dubu talatin duk sati ga jama’a karya ne.

Binciken har wayau ya gano cewa adireshin yanar gizon da aka bayar acikin labarin adireshi ne na bogi da ke yiwa tarko. Yan damfara ne suka tsara labarin dan zambatan jama’a. idan mutum ya latsa adireshin zai yadda aka wallafa wasu hotuna da nufin daukar hankali da kokarin gaskatawa mutane batun tallafin wadda kuma karya ne. domin karanta cikekiyar labara latsa nan

Shin Wani Kansila a Jahar Kano Ya Nada Mutane 18 a Matsayin Masu Taimaka Masa?

Masu bin diddigin labarai dan tantance sahihancin su na CDD sun gano wani labari da mai amfani da shafin Twitter ya wallafa a shafin sa. Yayi  tsokaci daya bayyana cewa wani zababben kansila a jahar Kano ya nada mutane 18 a matsayin masu taimaka a bangarori daban-daban. Tsokacin ya ce Kansilan ya nada mai taimaka masa a bangaren al’amuran addini da siyasa da kungiyoyin sakai da bada dauki, dama sakatare na musamman ga Kansilan.

Binciken da CDD ta gudanar game da maganar cewa wani Kansila a jahar Kano ya nada mutane 18 a matsayin masu taimaka masa ya gano cewa gaskiya Kansila ya nada mutanen 18 a matsayin mataimaka a gare shi.

Kansilan, Hon. Muslihu Yusuf Ali wanda ke wakiltar mazabar Guringawa a karamar hukumar Kumbutso da ke kewayen birnin Kano, a jahar Kano ya tabbatar wa CDD nadin mutane 18 din a matsayin mataimaka a gare shi. Domi karanta cikkayar labari latsa nan

Shin Ranar 15 ga Watan Maris, 2021 Mahaifin Dr. Ngozi Okonjo-Iweala Ya Rasu?

A ranar 15 ga watan Maris din shekara ta 2021, masu bincike da bin didddigin labarai dan gano sahihancin su na Cibiyar Bunkasa Demokaradiyya da Cigaba (CDD) sun gano wani labari da majiyoyi da Punch da ABN suka wallafa. Majiyoyin sunyi ikirarin cewa Farfesa Chukwuma Okonjo, wato mahaifin daraktar hukumar cinikayya ta duniya WTO, Dr. Ngozi Okonjo-Iweala ya rasu.

Haka nan rahotanni sun bayyana cewa wata sanarwa da Dr. Ngozi ta fitar a madadin iyalanta ta bayyana cewa baban ta, wadda shine mai ya rike sarautar Obi na Ogwashi-Uku na baya-bayannan a jahar Delta ya mutu ranar 15 ga watan Maris, 2021.

Sanarwar ta kara da cewa Farfesa Okonjo ya mutu yana mai shekara 91 a garin Legas jim kadan da dawowar sa daga kasashen Amurka da Ghana.

Binciken da CDD ta gudanar ya gano cewa labarin mutuwar Farfesa Chuwkuma Okonjo a ranar 15 ga Maris, 2021 din yana cike da rudani.

Tsohon basarake wadda ya rike mukamin Obi na Ogwashi Ukwu a jahar Delta ya mutu ne ranar 13 ga watan Satumban 2019 yana dan shekaru 91 a garin Legas.

CDD ta gano cewa lokacin da mahaifin Dr. Ngozi Okonjo-Iweala ya rasu ba a nada mukamin daraktar hukumar cinikayya ta duniya ba. Domin Karin ayai latsa nan

CDD na jan hankalin kafafen yada labarai da jama’a da su guji yada labaran karya ko wadan da basu da tabbacin sahihancin su. Kuna iya aikowa CDD labaran da kuke da shakku akansu dan tantance muku gaskiyar su ta hanyar aiko gajeren sako ko ta manhajar WhatsApp akan lamba: +2349062910568.

Wasu daga ciki labaran karya da CDD ta bankado tare da wallafa su

  1. gwamnatin tarayya ba ta saye manhajar whatsapp ba
  2. sheikh sharif ibrahim saleh bai soki dakatar da abduljabbar nasiru kabara daga waazi a kano ba
  3. ba a kori fulani a jahar kano ba
  4. shin masu zanga zanga sun mamaye titin zuwa filin jirgin saman abuja ranar 4 ga maris 2021
  5. hoton da aka ga shanu na cin timatir a gefen hanya ba a najeriya aka dauke shi ba

Center for Democracy and Development West Africa| CDD West Africa