Labaran Karya da CDD ta Gano Tare da Binciko Sahihancin Su a Mako na Biyu na Watan Maris, 2021

A mako na biyu na watan Maris din shekara ta 2021, masu bin diddigin labarai dan gano sahihancin su na Cibiyar Bunkasa Demokaradiyya da Cigaba (CDD) sun bankado tare da binciko gaskiyar wasu labaran karya da aka wallafa a kafafen sada zumunta na zamani irin su Facebook, Twitter da manhajar WhatsApp. Ga labaran nan kamar yadda wannan mujalla ta mu ta wallafa su:

Gwamnatin Tarayya Ba Ta Saye Manhajar WhatsApp Ba

Masu bin diddigin labarai dan gano sahihancin sa na Cibiyar Bunkasa Demokaradiyya da Cigaba (CDD) sun gano wani sako da aka wallafa a shafin Facebook da ke ikirarin cewa gwamnatin tarayyar Najeriya ta saye manhajar WhatsApp da ake amfani da ita wajen turawa da karbar sakonni.

Binciken da CDD ta aiwatar ya gano cewa gwamnatin Najeriya ba ta saye manhajar WhatApp din ba kamar yadda akayi ikirari. Karin binciken da CDD ta aiwatar ya gano cewa sakon da wanda wani mai lura da wani shafin Facebook mai suna “Best of Mazi Nnamdi Kanu” ya wallafa shi dandalin Facebook din ya riga ya aiyana shi a matsayin labarin bogi.

Ba zai yiwu Facebook su sayar da kamfanin da ta samar dashi akan zabar kudi dala biliyan goma sha tara da digo uku ($19.3 billion), da ke da mallakar hannun jari da kudin su yakai dala biliyan sha biyu ($12 billion), abu ne da bazai yiwu ba ace an sayar dashi akan naira biliyan uku (3BN)  kacal ga gwamnatin Najeriya.

Bayan gudanar da zuzzurfan bincike, CDD na tabbatar da cewa gwamnatin Najeirya ba ta saye manhajar WhatsApp ba kamar yadda sakon da aka yada a wasu shafukan sada zumunta na zamani ya bayyana. Domin karanta cikekken labarin latsa nan

Sheikh Sharif Ibrahim Saleh Bai Soki Dakatar Da Abduljabbar Nasiru Kabara Daga Wa’azi a Kano Ba

A ranar Alhamis, 4 ga watan Maris shekara ta 2021, masu binciken labarai dan tantance sahihancin su na Cibiyar Bunkasa Demokaradiyya da Cigaba (CDD) sun gano wata murya mai tsawon minti 9 da dakika 27 da aka nada kuma ake yadawa ta manhajar WhatsApp. Acikin muryar anyi dogon sharhi tare da sukar dakatar Malam Abdujjabar Nasiru Kabara daga gabatar al’amuran wa’azi a jahar Kano sakamakon cece-kuce da maganganun sa suka janyo. Wata gabatarwa da ake yadawa da muryar tace Sheikh Shariff Ibrahim Saleh Alhussain ne ya yi wannan jawabi.

Binciken da CDD ta gudanar ya gano cewa muryar da ake yadawa ta manhajar WhatsApp din ba ta Sheikh Shariff Ibrahim Saleh Alhussain ba ce. Hasalima Sheikh bai yi magana akan batun dakatar Abduljabbar ba balle ya soki al’amarin.  CDD ta tuntubi da ga Sheikh Shariff Saleh, wato Engr. Almuntasir Ibrahim Saleh Alhaussain ya kuma bayyana cewa muryar da ake yadawa din ba ta mahaifin sa ba ce. Domin karanta cikekken labarin latsa nan

CDD na jan hankalin kafafen yada labarai da jama’a da su guji yada labaran karya ko wadan da basu da tabbacin sahihancin su. Kuna iya aikowa CDD labaran da kuke da shakku akansu dan tantance muku gaskiyar su ta hanyar aiko gajeren sako ko ta manhajar WhatsApp akan lamba: +2349062910568.

Wasu daga ciki labaran karya da CDD ta bankado tare da wallafa su

  1. ba a kori fulani a jahar kano ba
  2. shin masu zanga zanga sun mamaye titin zuwa filin jirgin saman abuja ranar 4 ga maris 2021
  3. hoton da aka ga shanu na cin timatir a gefen hanya ba a najeriya aka dauke shi ba
  4. babu wani tsarin bada tallafi daga gidauniyar dangote
  5. bill gates bai ce zaa sake samun wata annoba bayan cutar korona ba