Kwamitin Gwamnatin Tarayya Kan Yakar Cutar Korona Bai Fitar Da Sanarwa Game Da Saka Dokar Kulle Ba

Tushen Magana:

A ranar 15 ga watan Janairun shekara ta 2021 masu tantance sahihancin labarai na Cibiyar Bunkasa Demokaradiyya da Cigaba (CDD) sun gano wani sakon da ake yadawa a manhajar WhatsApp, sakon na cewa kwamitin kar takwana na gwamnatin tarayya aka cutar Korona ya fitar da sakon game da sake kakaba dokar kulle  a fadin kasa.

Sakon y ace: “nan ba da dadewa ba, watakila ma a karshen makonnan za’a saka dokar kulle ta tsawon sati biyu”, karshen ya nuna wadda ya sa hannu wato: “Dr. Sani Aliyu” tare da ayyana shi a matsayin “shugaban kwamintin yaki da cutar Korona na gwamnatin tarayya”.

Gaskiyar Magana:

Masu tantance sahihancin labarai na CDD sun gano cewa ba kamar yadda sakon da aka yada din ya zayyana ba, Dr. Sani Aliyu ba shine shugaban kwamitin yaki da cutar Korona na gwmanatin tarayya ba, shugaban shine Boss Mustapha wadda kuma shine sakataren gwamnatin tarayya.

Har wayau, CDD ta samu wani bidiyo mai tsawon dakika 51 da kwamitin kar takwana kan cutar Korona na gwamnatin tarayya ya sake, acikin bidiyon, shugaban tsare-tsare na kwamitin, Dr. Sani Aliyu ya bayyana sakon da ake yadawa game da saka dokar kullen a matsayin labarin bogi yayin day a gargadi jama’a da su guji yarda sakon bogin da ake yadawa din.

Dr. Sani Aliyu kara da cewa, kwamitin gwamnatin tarayyar ya da sahihan hanyoyin da yake bi wajen yada bayani, ba yadda za’a kwamitin ya yada muhimmin sako da manhajar WhatsApp.

Kammalawa:

CDD na tabbatar da cewar jita-jitar da ake yadawa cewa kwamitin gwamnatin tarayya kan yakar cutar Korona ya fitar da sanarwa game kakaba dokar kulle karya ne. Wani bidiyo mai tsawon dakika 51 da mai kula da tsare-tsaren kwamitin, Dr. Sani Aliyu yayi magana acikin sa hujja ce akan haka. Sakon da ake yadawa ta manhajar WhatsApp game da dokar kullen sako ne na bogi.

CDD na jan hankalin jama’a da su rika tantance sahihancin labarai kafin yada su ga sauran mutane a kowane lokaci.

#AgujiYadaLabaranBogi

Center for Democracy and Development West Africa| CDD West Africa