Skip to main content

Kudin Najeriya Bashi Ne Yafi Rashin Daraja a Nahiyar Afirka Ba

Tushen Magana:

A ranar 21 ga watan Afirilun shekara ta 2021, masu tantance sahihancin labarai na Cibiyar Bunkasa Demokaradiyya da Cigaba (CDD) sun gano wani rahoto da aka wallafa da ya dauki hankalin jama’a da kuma akayi ta cece-kuce a kansa, rahoton yace kudin Najeriya, wato Naira itace tafi kowane kudi rashin daraja a nahiyar Afirka

Rahoton wanda aka yadashi a kafafen sada zumunta na zamani da suka hada da manhajar WhatsApp ya zayyano tare da kwatanta darajar kudaden kasashe nahiyar Afirak 25 da Naira. Bayan wannan kwatance, rahoton ya bayyana cewa kudin ksara Angola da ake kira Kwanza da na Madagascar mai suna Ariary da na Sudan mai suna Pound duk sunfi Naira daraja.

Kamar yadda rahoton ya kara yin ikirari, Kwanza 1 da kasar Angola ya an zaman Naira 12, Ariary na Madagascar ya na zaman Naira 14 yayin da Pound 1 na Sudan ke zaman Naira 42 ta Najeriya.

Gaskiyar Al’amari:

Binciken da CDD ta gudanar game da kasancewar Naira a matsayin kudin da yafi kowane kudi rashin daraja a nahiyar Afirka ya gano cewa rahoton ya na dauke da rudani da jirkitarwa.

Masu tantance sahihancin bayanai na Cibiyar Bunkasa Demokaradiyya da Cigaba (CDD) sun auna darajar Naira da sauran kudaden kasashen da rahoton ya zayyano. Nazarin CDD ya gano cewa Kwanza 1 na kasar Angola ya na matsayin kasa da Naira 1 ne, wannan kuma ya karyata ikirarin da rahoton yayi ne tun farko cewa Kwanza 1 ya na zaman Naira 12 ne. Ariary 1 na kasar Madagascar shima ya na zaman kasa da Naira ne ba kamar yadda rahoton yace ba. Pound 1 na Sudan ya na matsayin Naira 1 ne ba kamar yadda akace acikin rahoton ba cewa yana matasyin Naira 42.

Kammalawa:

Bincike da nazarin da CDD ta gudanar ya gano cewa wani rahoton da ake yadawa a kafafen sada zumunta na zamani cewa kudin Najeriya wato “Naira” itace mafi rashin daraja a nahiyar Afirka karya ne.

CDD na jan hankalin jama’a kan tantance sahihancin labari kafin yada shi ga sauran mutane.

Kuna iya aikowa CDD labaran da kuke da shakku akan su dan tantance muku gaskiyar su ta hanyar aiko gajeren sako SMS ko ta manhajar WhatsApp akan lamba +2349062910568 ko a shafin Twitter ta wannan adireshi: @CDDWestAfrica

#AgujiYadaLabaranBogi

CDD na shawartar kafafen yada labarai kan zurfafa bincike da tattara gaskiya labarai kafin wallafa su. Haka nan ana jan hankalin jama’a kan tantance sahihancin labari kafin yada shi ga sauran mutane.

Kuna iya aikowa CDD labaran da kuke da shakku akan su dan tantance muku gaskiyar su ta hanyar aiko gajeren sako SMS ko ta manhajar WhatsApp akan lamba +2349062910568 ko a shafin Twitter ta wannan adireshi: @CDDWestAfrica

#AgujiYadaLabaranBogi

Center for Democracy and Development West Africa| CDD West Africa