Joe Biden Bai Umarci Hukumar Shigi da Ficin Amurka Ta Bada Izinin Aiki Da Zama Ta Yanar Gizo Ga Yan Najeirya Ba

Gaskiyar Magana: Karya Ne!

Tushen Magana:

Akwai wata sanarwa da ake yadawa a kafafen sada zumunta na zamani da suka hada da manhajar WhatsApp da ke cewa Shugaban kasar Amurka, Joe Biden ya bada umarnin daukar yan Najeriya aiki ta hanyar yanar gizo tare da basu takardar izinin zama a kasar ta Amurka.

Sanarwar wadda aka yi ikirarin cewa wani bangare na takardar da aka rabawa manema labarai ance ta fito ne daga ofishin da ke kula da yan kasar Amurka da harkokin shigi da fici kuma Shugaba Biden ya sanyawa dokar dake bada izini dan daukar yan Najeirya aiki ta hanyar yanar gizo tare da basu takardun izinin zaman kasar Amurka

A cewar wannan sanarwa da ake yadawa a kafafen sada zumunta na zamani an mika kwafin wannan takardar sanarwa ga ofishin jekadancin Najeriya da ke Amura kuma ranar da za a rufe neman daukar aikin tare da bada izinin zama a kasar ta Amurka ga yan Najeirya itace 30 ga watan Afirilu, 2021.

Gaskiyar Magana:

Binciken da CDD ta gudanar akan shafin yanar gizo na ofishin kula da yan kasar Amurka da shigi da fici U.S Citizenship and Immigration Services ya gano cewa babu wata sanarwa da ta fito daga wannan ofishi.

Wata alama da ke bayyana cewa sanarwar ta bogi itace sanarwar tana kunshe da kura-kuari masu yawan gaske haka nan babu wata hujjar cewa Shugaban Amurka Joe Biden ya saka hannu domin bada izini dan daukan yan Najeriya ta hanyar yanar gizo ko wani izinin zama ga yan Najeriya din a wannan lokaci.

Har wayau ofishin jekadancin Amurka da ke Najeriya ya yi watsi da sanarwar ta cikin wani bayani da ya wallafa a amintaccen shafin sa na Twitter (@USinNigeria). Ofishin ya bayyana cewa sanarwar sanarwa ce ta bogi da aka tsara dan damfarar jama’a.

Bayanin ofishin jekadancin Amurkan ya kara da cewa: “Ayi hankali da aikin yan damfara! Mazambata da yan damfara na yada wata sanarwar bogi da ke ikirarin bada sabon izinin zama da yin aiki a Kasar Amurka ga yan Najeriya da ke tsakanin shekaru 40 zuwa 55. Wannan tsohuwar sanarwa ce ta bogi wadda aka canzawa fasali, ku kula da kyau kada a zambace ku!”-inji bayanin da ofishin jekadancin Amurka a Najeriya ya wallafa a shafin sa na Twitter.

Tun bayan kama aiki, sabon Shugaban Amurka Joe Biden ya sanya hannu kan dokoki da dama da suka shafi harkokin shigi da fici na tsohon Shugaba Donald Trump.

Yana da kyau a sani cewa babu daya daga cikin dokokin da Shugaba Biden ya sanyawa hannu da ta shafi daukar yan Najeriya aiki ta hanyar yanar gizo ko basu izinin zama a Amurka.

Kammalawa:

Shugaban kasar Amurka Joe Biden bai bada umarnin bada izinin zama dan yin aiki a Amurka ta hanyar yanar gizo ba. Wata sanarwa da ake yadawa ta kafafen sada zumunta na zamani da ke ikirarin haka sanarwa ce ta bogi.

CDD na tabbatar da cewa wannan sanarwa wasu yan damfara ne suka tsara ta dan zambatan yan Najeriya, dan haka jama’a suyi watsi da ita.

Kuna iya aikowa CDD labaran da kuke da shakku akansu da gano muku gaskiyar su. Za ku iya turo gajeren sako (SMS) ta manhajar WhastApp akan lamba: +2349062910568 ko ku tuntube mu a shafin Twitter a @CDDWestAfrica.

#AgujiYadaLabaranBogi

Center for Democracy and Development West Africa| CDD West Africa