Tushen Magana:

A ranar Juma’a, 4 ga watan Disamban shekara ta 2020, masu tantance sahihancin labarai na Cibiyar Bunkasa Demokaradiyya da Cigaba (CDD) sun gano wani labari da aka wallafa kuma ake yadawa musamman a kafafen sada zumunta na zamani. Labairn yace jam’iyyar APC a jahar Kano ta tsige shugaban ta Hon. Abdullahi Abbas daga shugabancin jam’iyyar. Kafafen da suka rawaito labarin sun hada Labarai24 da ArewaBlog.

Labarin tsige Hon. Abbas din ya karade dandalin Facebook dama WhatsApp inda aka dauki hoton labarin kuma aka rika wallafawa a zaurukan wadannan dandalolin sada zumunta da muhawara na zamani.

Gaskiyar Magana:

Kawo lokacin wallafa wannan tantancewa da CDD ta aiwatar akan labarin da misalign karfe 2 na rana ranar Ladi, 6 ga watan Disanban shekara ta 2020 babu wata takarda ko sanarwa da aka gabatarwa ga shugaban jam’iyyar APC din a Kano, Hon. Abdullahi Abbas.

Har wayau babu wata sanarwa da jam’iyyar APC din ta fitar game da tsige shugaban nata.

Da CDD ta tuntube shi game da batun, kakakin jam’iyyar a Kano, Hon. Sidi Mustapha Karaye ya bayyana maganar tsige shugaban jam’iyyar a matsayin labarin bogi.

Hon. Karaye yace: “Har yanzu Hon. Abdullahi Abbas ne shugaban jam’iyyar APC a Kano, babu daya daga cikin jagogorin jam’iyyar da ya rubuto ko sanar da jam’iyyar cewa an tsige shugaban jam’iyyar”.

“Munji wai a radio wai an tsige shigaban jam’iyya, amma nine mai magana da yawun jam’iyyar kuma bani da wannan labari, ta yaya wannan labari zai zama gaskiya? Wannan ba wani abu bane illar labarin bogi da muma bamu san inda ya fito ba”

“Ina san na tabbatar maka da cewa wannan labari ne na karya tunda a hukumance bamu da wani bayani mai kama da haka”, inji kakakin jam’iyyar APC a Kano.

Kammalawa:

Labarin da ake yadawa cewa jam’iyyar APC a Kano ta tsige shugaban ta Hon. Abdullahi Abbas daga shugabanci karya ne. Har zuwa ranar Ladi, 6 ga watan Disamban shekara ta 2020 Hon. Abdullahi Abbas ne shugaban jam’iyyar tunda babu umarni ko sanarwar tsige shi kamar yadda kakakin jam’iyyar ya tabbatar wa CDD.

CDD tana jan hankalin jama’a game da yada labaran da basu da tabbacin sahihancin su. Kuna iya aikowa CDD labaran da kuke shakku akansu dan tantance muku ta hanyar WhatsApp ko gajeren sako ta wannan lamba +2349062910568 ko a shafin Twitter a: @CDDWestAfrica ko @CDDWestAfrica_H

#AgujiYadaLabaranBogi

Center for Democracy and Development West Africa| CDD West Africa