Iska Bata Lalata Sabuwar Kwalta a Jahar Abia Ba a Ranar Talata, 8 ga Satunba, 2020

Tushen Magana:

A ranar Talata, 8 ga watan Satunban shekara ta 2020 wani adireshi mai lakabi da @Gen_Buhar a dandalin Twitter ya wallafa labarin cewa wata iska ta lalata wata sabuwar hanya da aka kammala ta a jahar Abia dake kudancin Najeriya.

Kawo lokacin hada wannan tantancewa wannan labari mutane kimanin 225 ne sukace lamarin ya burgesu yayin da wassu mutanen 163 suka kara yadashi, har wayau wassu mutane 76 sunyi tsokaci game da labarin.

Gaskiyar Magana:

Binciken da CDD ta gudanar ya gano cewa hotunan aka wallafa labarin dasu sun samo asali ne daga kasar Thailand.

Binciken na CDD wanda yayi anfani da tsarin Google Reverse Image Search ya gano cewa hoton da akayi anfani dashi din daya ne daga cikin tarin wassu hotuna da Thansettakij ya wallafa.

Kammalawa:

Wani labari da aka wallafa a shafin Twitter da yayi ikirarin cewa iska ta lalata wata kwalta aka samar a jahar Abia karya ne.

Cibiyar Bunkasa Demokaradiyya da Cigaba (CDD) tana jan hankalin mutane da akowane lokaci su rika tantance sahihancin labari kafin yadashi.

Kuna iya aikowa CDD labaran da kuke da shakku akansu dan tantance muku ta wannan lamaba: +2349062910568 or ko ta shafin Twitter: @CDDWestAfrica ko @CDDWestAfrica_H

#AgujiYadaLabaranBogi

Center for Democracy and Development West Africa| CDD West Africa