Skip to main content

Tushen Magana:

Wani saki dake cigaba da yaduwa a manhajar WhatsApp ya kalubalanci gwamnatin tarayyar Najeriya da boye gaskiya game da cutar Corona a kasar. Wannan sako an danganta shi da injiya mace ta farko a Najeriya wato Mrs. Olu Maduka.

Wassu daga cikin zarge-zargen da aka danganta su da Mrs. Maduka sun hada da cewa da yawa daga cikin masu dauke da cutar Corona suna cikin halin rai-kwakwai mutu-kwakwai dama wani jariri dan wata daya da haihuwa dake dauke da cutar Corona din.

Acikin sakon an bayyana cewa Mrs. Maduka tayi kuka game da halin da wannan jariri yake ciki. Har wayau wannan sako ya bayyana cewa kaso goma daga cikin adadin bullar cutar Corona da gwamnati ke bayyanawa ne kawai gaskiya.

Wannan sako da aka danganta shi da Mrs Maduka ya kara da cewa taga gawawwaki guda takwas (8) acikin awa daya lokacin da takai ziyara asibitin Mainland dake garin Legas.

Gaskiyar Magana:

Acikin wani martani da ta mayar ta hanyar wani faifan bidiyo data nada ta turawa masu tantance sahihancin labari na Cibiyar Bunkasa Demokaradiyya Da Cigaba (CDD), Mrs. Maduka tayi watsi da sakon da aka danganta ta dashi.

Kamar yadda ta zayyana, ta dade tana zaune a gida kafin ma a aiyana dokar zama a gida saboda haka maganar takai ziyara asibitin Mainland bata ma taso ba.

Mrs. Maduka ta bayyana karara cewa: “ina jawo hankalin mutane da cewa bani da alaka da sakon da ake yadawa game dani, bani na rubuta shi ba, bankai ziyara kowane gurin killace mutane ba ko asibitin Mainland ko ko’ina ma, hasali ma na kwashe kusan kimanain sati biyar ba tare da na fita ko ina ba”.

Mrs. Maduka ta cigaba da cewa, “bisa la’akari da shekaru na, ko kafin a kafa dokar hana fita waje bana zuwa ko’ina saboda shekaru na, dan haka banje kowane asibiti ba ko wani wajen killace mutane”.

Mrs. Maduka ta shawarci jama’a das u rika anfani da kafafan sada zumunta na zamani ta hanyoyin da suka kamata su kuma guji aikata abubuwa munana.

A jahar Legas dai ansamu bullar cutar Corona har sau 931, wannan adadi kuma shine mafi yawa tun bayan gano cutar a Najeriya a watan Fabrairun shekara ta 2020.

Gwamnan jahar Legas din, Babajide Sanwo-Olu yana cigaba da bada bayanai akan cutar a kodayaushe dama yunkurin da gwamnatin sa keyi wajen dakile yaduwar cutar a jahar baki daya.

Kammalawa:

Sakon da ake yadawa ta manhajar WhatsApp cewa Mrs. Maduka tace gwamnati na boye gaskiyar lamari game da cutar Corona karye. Ba itace ta rubuta sakon ba kuma bata ziyarci kowane asibiti ko wajen killace mutane ba ballatana ma tayi wani jawabi. CDD tana kira ga jama’a da suyi watsi da sakon tare da daina yadashi dama kirikira ko yada labaran karya.

#AdainaYadaLabaranKarya

Leave a Reply