Hukumar Tsaron Farin Kaya ta SSS Bata Kama Fasto Chris Ba Game Da Furucin Sa Akan 5G

Tushen Magana: A ranar 8 ga wata Maris din shekara ta 2020 Cibiyar Bunkasa Demokaradiyya da Cigaba wato CDD ta gano cewa anata yada maganganu a yanar gizo cewa hukumar tasaron farin kaya ta kasa wato SSS ta kama jagoran Majami’ar Christ Embassy wato Fasto Chris Oyakhilome.

Kamar yadda wani rahotannin suka bayyana, an cafke Faston ne sakamakon furucin sa na ruda jama’a game da tsarin yanar gizo mai sauri na 5G cewa yana alaka da Cutar Corona  ko COVID19.

Jawabin Faston mai cike da cece-kuce an yadashi ga miliyoyin mutane a satin da ya gabata a shafin sada zumnuta na Facebook kamar haka

Gaskiyar Magana:

Chris Oyakhilome shine ya samar kuma yake jagorantar majami’ar da mafiya yawan masu bauta acikinta matasa ne mai suna LoveWorld Incorporated da kuma ake kira Christ Embassy mai matsuguni a garin Legas da kuma take da rassa a duk fadin duniya baki daya.

Wani mai  sharhi akan al’amuran yau da kullum kuma rubuta a shafin jarida mai suna Fredrick Nwabufo ya wallafa wata kasida a ranar 7 ga watan Maris din 2020 inda yayi kira ga hukumomi da su kama malamin addinin.

Nwabufo ya kara tsokaci dangane da jan kafa wajen kama Fasto Oyakhilome da gwamnatin Najeriya take yi acewarsa karkashin dokar laifuffukan da ake aikatawa a yanar gizo.

Bayan janwo cece-kuce da wannan magana tayi, da yawan mawallafa a yanar gizo sunyi rubuce-rubuce na cewa ankama malamai addinin.

A wani martani dangane da batun, hukumar jami’an tsaron farin kayan ta Najeriya tace bata kama Fasto Oyakhilome ba.

Mai magana da yawun hukumar SSS din, Dr. Peter Afunanya ya jaddada cewa hukumar tsaron farin kayan bata kama Faston ba, ya kara da cewa: “DSS bata kama Fasto Oyakhilome ba”

Dan kara tantance wannan batu, masu tantance gaskiya ko rashin gaskiyar labarai na CDD sun tattauna da daya daga cikin manyan masu ibada a majami’ar Christ Embassy inda ya tabbatar musu da cewa jita-jitar kama Fasto Chris karya ne.

Jami’in majami’ar wanda ya bukaci a sakaye sunansa yace: “ina mai tabbatar muku da cewa minti gima sha biyar (15) da suka wuce mukayi mitin ta yanar gizo da Fasto Chris. Saboda haka wane Fasto Chris din aka kama?

Kammalawa:

Hukumar tsaron farin kaya ta SSS bata kama Fasto Chris Oyakhilome ba. Jita-jita ne marar tushe ne kawai mutane ke yadawa cewa an kamashi. CDD da hukumar wayar ka kan jama’a ta kasa NOA suna shawartan mutane da su rika tantance labari kafin yadashi.

#AdainaYadaLabaranKarya

Leave a Comment

Your email address will not be published.