Hukumar Lafiya Ta Duniya Bata Yada Sako Dangane Da Samuwar Maganin Cutar Corona Ba!

Tushen Magana:

A ranar 20 ga watan Agustan shekara ta 2020, masu tantance sahihancin na Cibiyar Bunkasa Deomkaradiyya da Cigaba suka gano wata makala da Myafricatoday ta wallafa inda tace hukumar lafiya ta duniya WHO ta fitar da wani muhimmin sako game da maganin cutar Corona.

Labarin wanda mai taken: “labari da dumi-dumin sa, WHO tana da muhimmin sako ga duniya game da maganin cutar Corona kamar yadda babban sakataren hukumar lafiyar Tedros Ghebreyesus  ya bayyana. WHO ta kara nazari akan binciken da akayi dan gano maganin cutar ta Corona”.

Kamar yadda labarin ya zayyana, WHO tana aiki kafada-da-kafada da gwamnatocin kasashen duniya dan ganin maganin cutar samu a ko’ina kuma ga dukkan jama’a.

Labarain ya kara da cewa matsayin da hukumar lafiya ta duniyar ta dauka yazo ne sakamakon wassu kasashe na yunkurin samar da maganin cutar dan sayar dashi a farashi mai tsada ga kasashen masu rauni.

Gaskiyar Magana:

Hukumar lafiya ta duniya WHO bata fitar da kowace sanarwa ko sako game da samuwar maganin cutar Corona ba. Nazarin da CDD ta gudanar akan labarin ya gano cewa babu inda aka zayyana “sakon” da ake cewa WHO din ta fitar acikin labarin da zauren yanar gizon ya wallafa, wannan kuma alama ce mai karfi wajen bayyana labarin a matsayin na bogi.

Hay wayau a ranar 4 ga watan Agustan shekara ta 2020, Dr Ghebreyesus yayin jawabi game cutar ta Corona ya bayyana ire-iren kalubalen da ake fuskanta wejen ganin bayan cutar da ta addabi duniya.

Wani binciken da CDD ta aiwatar ya kara gano cewa kwana daya bayan jawabin shugaban hukumar lafiya ta duniyar, Fafaroma Francis ya jaddada muhimmancin samuwar maganin cutar dan kaiwa ga dukkan jama’a

Fafaroma Francis yace: “zai zama abin takaici idan aka maida hankali wajen samo maganin cutar Corona da anfanin mawadata ko kuma ace wata kasa tana dashi wata bata dashi, kamata yayi a samar da maganin dan anfanin dukkan duniya”.

A wani sakon day a wallafa a shafin sa na Twitter, Dr Ghebreyesus yace lallai na aminta da maganar, mai girma Fafaroma”.

Wani binciken da CDD ta aiwatar ya gano cewa kadan daga cikin kanfanonin sarrafa magunguna ne suka daf-da kaiwa mataki na uku a yunkurin su na samun yardar samar da maganin cutar Corona.

Kammalawa:

Hukumar lafiya ta duniya WHO bata fitar da kowace sanarwa ko sako game da samuwar maganin cutar Corona ba. Nazarin da CDD ta gudanar akan labarin ya gano cewa babu inda aka zayyana “sakon” da ake cewa WHO din ta fitar acikin labarin da zauren yanar gizon ya wallafa, wannan kuma alama ce mai karfi wajen bayyana labarin a matsayin na bogi.

CDD tana kira ga jama’a da suyi watsi da wannan ikirarin tare da karfafa musu gwiwa wajen tantance sahihancin labari kafin yadashi.

Kuna iya aikowa CDD labarai dan tantance sahihancin su ta wannan lamba: +2348062910568 ko ta shafin mu na Twitter a: @CDDWestAfrica ko @CDDWestAfrica_H

#AgujiYadaLabaranKarya

Center for Democracy and Development West Africa| CDD West Africa

Leave a Comment

Your email address will not be published.