Hukumar Kula Da Ingancin Abinci da Magunguna Ta Amurka Bata Amince Da Hydroxychloroquine Dan Magance Cutar Corona Da Sauran Cututtuka Ba

Tushen Magana:

Wani sako da ake cigaba da yadawa a dandalin WhatsApp ya bayyana cewa Hydroxychloroquine, Azithromycin da Zinc Sulphate sunadarai ne da zasu magance cutar Corona.  Kamar yadda sakon ya bayyana, hadakar wadannan magunguna uku baraza ne kuma magani daga cutar Corona kamar yadda hukumar kula da ingancin abinci da magunguna ta kasar Amurka ta bayyana.

Wani sashi na sakon ya bayyana cewa: “hukumar kula da ingancin abinci da magunguna da kasar Amurak da ake kira USA Food and Drug Administration (FDA) a turance ta amince da maganin”

Gaskiyar Magana:

Wannan sako da ake yadawa yana da alaka da wani bidiyo da shima aka yadashi a kafafen sada zumunta na zamani inda wata likita yar asalin Najeriya Stella Immanuel tayi ikirarin samo maganin cutar Corona.

Acikin bidiyon, Stella Immaneul tayi ikirarin cewa ta samo maganin cutar Corona kuma maganin shine Hydroxychloroquine da Azithromycin da Zinc Sulphate.

Yayin da take jawabi acikin bidiyon, Stella wadda take tare da wassu da ake ganin abokan aikinta ne tace ta kula da mutane da yawan siu ya zarta 350 da hamsin masu dauke da cutar Corona da wadannan magungunan da ta anbata kuma wassu daga cikin su suna dauke da cutar hawan jini da ciwon suga sannan da yawan su tsofi ne.

Stella ta kara da cewa, wadda tafi kow yawan shekaru acikin mutanen da ta warkar shekarun ta 92 kuma Hydroxychloroquine da Zinc da Zithromax ne ta bata kamar yadda sune magugunan da baiwa sauran masu dauke da cutar Corona.

Saidai ba kamar yadda sakon WhatsApp din ya yayata ba cewar FDA ta amince da magungunan a matsayin maganin cutar Corona, hukumar kula da ingancin abinci da magunguna ta kasar Amurka wato Food and Drug Administration tama dakatar da umarnin da ta bayar na anfani da sinadaran chloroquine da hydroxychloroquine dan magance cutar Corona, wannan umarni an badashi tun watan Maris din shekara ta 2020.

FDA tace ta damu irin tasiri ko rashin tasirin da maganin zayi ga lafiyar mutane musamman yanzu da jama’a ke te yadawa bayanai cewa shine maganin cutar Corona.

“bayan la’akari da anfani da rashin anfanin wadannan magungunan, bayanai sun kankama cewa gudummawarsu ga lafiya bata da yawa, saboda haka aka bada umarnin dakatar da anafin dasu dank are lafiyar jama’a, inji FDA”

Har wayau a ranar 15 ga watan Yulin shekara ta 2020, FDA ta fitar wata sanarwa inda ta fitar da matsayar ta.

FDA tace bisa nazari da binicken kimiyya da suka bayyana ta dakatar da anfani da hydroxychloroquine da chloroquine dan anfani dasu wajen bada agaji ko kulawa ga masu dauke da cutar Corona. Daukar wannan mataki ya biyo bayan hujjojin dake nuna rashin tasirin hydroxychloroquine da chloroquine wajen rage mace-macen dake faruwa sakamakon cutar Corona dama rage kaifin cutar ajikin masu dauke da ita.

Itama gwamnatin Najeriya ta sanar da cewa hydroxychloroquine da chloroquine suna matakin binciken kimiyya dan gano ko suna iya magance cutar ta Corona ko a’a, kuma kwararru a fannin lafiya suna ta gwaje-gwaje a dakin auna magunguna dan bincike akan wadannan sinadarai guda biyu. Shima a nasa jawabin a ranar 21 ga watan Maris din shekara ta 2020, Ministan lafiya ya bayyana hukumar kula da ingancin abinci da magunguna ta kasa National Agency for Food and Drug Administration and Control (NAFDAC) na cigaba da gudanar da bincike akan maganin zazzabin cizon sauro.

Ehanire ya kara da cewa: “binciken tantance inganci ko aikin magani yakan dauki lokaci. Muna cigaba da gwajin maganin akan marasa lafiya tare da tattara bayanai. Bazan iya fadar yaushe ne sakamako zai fita ba saboda ahalin yanzu bincike da cigaba da gudana”.

Kammalawa:

Labarin da ake yadawa cewa Hydroxychloroquine da Zinc da Zithromax suna maganin cutar Corona karya ne! Hakanan hukumar kula da ingancin abinci da magunguna ta kasar Amurka Food and Drug Administration (FDA) bata amince da wadannan sinadarai ba a matsayin magungunan cutar Corona kamar yadda ake yayatawa.

CDD tana jan hankalin mutane game da yada labaran karya tare da yin takan tsantsan wajen yadda da dukkan wani magani da bai samu amincewar hukumomin lafiya ba.


Ku kiramu akan lamba: +2349062910568 ko ku tuntube mu a shafin mu na Twitter a: @CDDWestAfrica ko @CDDWestAfrica_H

#AgujiYadaLabaranBogi.

Center for Democracy and Development West Africa| CDD West Africa

Leave a Comment

Your email address will not be published.