Hukumar Hisbah a Jahar Kano Bata Ci Tarar Daliban Jami’ar Bayero N20,000 Ba

Tushen Magana:

A ranar 6 ga watan Afirilun shekara ta 2021, wani ya bulla daga kafafen yada labarai na yanar gizo da yawa. Labarin ya ce Hukumar Hisbah ta jahar Kano ta ci tarar daliban Jami’ar Bayero maza da mata naira dubu ashirin (N20,000) kowannen su sakamakon kama su da laifin zama a daki daya duk da kasancewar sub a ma’aurata ba.  Majiyoyi sun hada da: Sahara ReportersTori.ngKanyiDailyNigerDeltaConnectNaijaNewsAllSchoolsForum.

Labarin ya ce: “Hukumar Hisbah a Jahar Kano ta Bukaci Daliban Jami’ar Bayero Maza da Mata Su Biya N20,000 Dan Yin Belin Kansu Bayan Aikata Laifin Zama a Daki Guda”

Gaskiyar Magana:

Binciken da CDD ta gudanar akan labarin cin tarar daliban da aka ce Hukumar Hisba a jahar Kano tayi karya ne. Tun farko majiyoyi da yawa rawaito cewa Hisbah ta damke daliban ne sakamakon zama a daki daya duk da kasancewar su ba ma’aurata ba, sakamakon haka a cewar labarin Hisbah taci tarar daliban naira dubu ashirin (N20,000) kowannen su.

Da yake yiwa CDD bayani akan batun, mai magana da yawun Hukumar Hisbah ta Jahara Kano, Lawan Ibrahim Fagge ya bayyana labarin a matsayin na bogi, ya kara da cewa Hukumar Hisbah bata ci tarar kowa ba.

Fagge ya ce Hisbah ba kotu bace, dan haka bata cin tarar mutane.

Lawan Ibrahim Fagge ya kara da cewa: “wannan labari ne na karya, Hisbah bata ci tarar kowane dalibi ba. Jama’ar da ke rayuwa a inda daliban suke ne suka tuntubi Hukumar Hisbah game da yadda daliban Musulmai ke rayuwa a daki daya kuma ba ma’aurata bane, daga nan sai Hisbah ta gana da daliban tare da basu shawara game da rashin dacewar hakan”

“abinda Hisbah tayi shine ganawa dasu tare da yi musu nasiha da basu shawara amma kawai sai ga labari ya bulla cewa wai mun kama tare da cin tarar daliban, wannan karya ne. Babu tarar wadda muka ci”

Kammalawa:

Labarin da ake yadawa cewa Hukumar Hisbah a jahar Kano ta ci tarar daliban Jami’ar Bayero maza da mata da ta samu suna zama a daki daya naira dubu ashirin (N20,000) kowannen su karya ne. Hisbah bata ci tarar kowane dalibi ba. Labarin da ke yayata cin tarar daliban labari ne na bogi.

CDD na shawartar kafafen yada labarai kan zurfafa bincike da tattara gaskiya labarai kafin wallafa su. Haka nan ana jan hankalin jama’a kan tantance sahihancin labari kafin yada shi ga sauran mutane.

Kuna iya aikowa CDD labaran da kuke da shakku akan su dan tantance muku gaskiyar su ta hanyar aiko gajeren sako SMS ko ta manhajar WhatsApp akan lamba +2349062910568 ko a shafin Twitter ta wannan adireshi: @CDDWestAfrica

#AgujiYadaLabaranBogi

Center for Democracy and Development West Africa| CDD West Africa