Hukumar Fasakwafri ta Kasa Bata Bada Sanarwar Barazanar Tsaro a Babban Birnin Tarayya Abuja Ba.

Tushen Magana:

A ranar Asabat, 5 ga watan Satumban shekara ta 2020, masu tantance sahihancin labarai na Cibiyar Bunkasa Demokaradiyya da Cigaba (CDD) sun gano wata wasika da ake yadawa a dandalin WhatsApp inda kayi ikirarin cewa hukumar fasakwafri ta kasa wato Nigeria Customs Service a turance ta wallafa wani sako dake bayyana barazanar tsaro dake fuskantar babban birnin tarayya Abuja da kuma mazauna cikin birnin.

Sakon wanda aka wallafi ta fasalin PDF yayi ikirarin cewa wassu bayanan sirri da suka shafi tsaron kasa da shugaban hukumar fasa kwafrin ta kasa sun bayyana akwai sansanonin yan kungiyar tada kayar baya ta Boko Haram acikin da kewayen babban birnin tarayya Abuja.

Sakon wanda aka rubuta shi a takarda mai dauke da hatimi da alamun hukumar fasa kwafrin ta kasa yace yan Boko Haram suna shirya kai hare-hare a yankuna Abujan. Sakon ya kara da cewa yan kungiyar Boko Haram suna da sansanoni har guda biyar a kewayen babban birnin tarayya Abuja da Nasarawa da jihar Kogi.

Gaskiyar Magana:

Binciken da CDD ta gudanar ya gano cewa hukumar fasa kwafri ta kasa bata wallafa ko yada kowane irin sako ba game da fargabar tsaro ko bada wani gargadi bag a mutane dake rayuwa a Abuja da kewayen ta.

Da yake yiwa CDD bayani game da batun, jami’in yada labarai da hulda da jama’a na hukumar fasakwafrin ta kasa, Joseph Attah, yace hukumar sa bata inda wannan takarda dama sakon da take dauke dashi suka samo asali ba.

Attah ya kara da cewa: “bamu san inda wannan takarda ta sami asali ba, idan akwai wata barazanar tsaro ba ta wannan hanya za’a isar da sako ga mutane ba, tsaro abune mai muhimmanci”.

Suma da suke mayar da martani cikin gaggawa game da batun, rundunar tsaro ta kasa ta cikin wata sanarwa da mai lura da harkokin yada labarai na rundunar  Major John Eneche ya sanyawa hannu ta bada tabbacin wanzuwar zaman lafiya da tsaro ga dukkan jama’a.

Eneche yace dukkan rundunonin tsaro suna cigaba da sa ido dan tabbatar kariya walwalar jama’a kuma jami’an tsaro sun rubanya yunkurin su na tabbatar da tsaro.

Kammalawa:

Hukumar kula da fasakwafri ta kasa bata wallafa kowane irin sako ba game da barazanar tsaro aciki da kewayen babban birnin tarayya Abuja. Mai magana da yawun hukumar ta kwastam ya bayyanawa CDD cewa basu san inda sakon da ake yadawa ta dandalin WhatsApp dake cewa yan Boko Haram sun mamayi birnin Abuja ba.

CDD tana kira ga jama’a da suyi watsi da wannan sako saboda rashin sahihancinsa tare da tantance sahihancin labarai kafin yadasu.

Kuna iya aikowa CDD sakonni ko labaran da kuke da shakku akansu dan tantance muku ta wannan +2349062910568 lamba ko ta shafin na Twitter a @CDDWestAfrica ko @CDDWestAfrica_H

#AgujiYadaLabaranKarya

Center for Democracy and Development West Africa| CDD West Africa