Hoton Dake Yawo a Kafafen Sada Zumunta na Zamani Na Wata Mata Cikin Jini Nade a Tutar Najeriya Hoto Ne Bogi!

Tushen Magana:

A ranar Laraba, 21 ga watan Oktoban sheraka ta 2020, masu tantance sahihancin labarai na Cibiyar Bunkasa Demokaradiyya Da Cigaba (CDD) sun gano wani hoto na wani mutum dake dauke da gawar wata mata da dake cikin jinni da aka nade da tutar Najeriya.

Hoton wanda yaja hankalin mutane da yawan gaske musamman a dandalin sada zumunta na zamani ya samu kimanin mutane 105,700 da suka nuna goyon bayansu gare shi yayinda wassu mutanen 6,934 suka tofa albarkacin bakin su.

Bayanin da hoton ke dauke dashi ya nuna cewa matar ta rasa ranta ne yayin da aka budewa masu zanga-zangar #EndSARS a Lekki Toll Gate dake garin Legas wuta.

Gaskiyar Magana:

Binciken da CDD ta gudanar ya gano cewa hoto bashi da alaka da harbe-harben da akayi a Lekki Toll Gate.

CDD har wayau ta gano cewa matar da wani mutum ke dauke da ita cikin jinni a nade acikin tutar Najeriya wani sashi ne na wani fim da aka shirya kuma aka dauka a jahar Akwa Ibom dangane da cikar Najeriya shekaru 60 da samun mulkin kai.

Sunan fim din “Lord, Heal Our Nation” kuma kungiya kiristoci masu yiwa kasa hidima wato Nigerian Christian Corpers’ Fellowship (NCCF) ne suka shirya shi.

A wata sanarwa da kungiyar ta fitar a ranar 22 ga watan Oktoban shekara ta 2020 tace hoton ba’a harbe-harben da ya faru Lekki Toll Gate aka daukeshi ba kamar yadda jita-jitar ta yada.

Hakanan Onyinye Francis, daya daga cikin wadan da suka taka rawa acikin shirin fim din tace matar da ake yada hoton nata tananan kalau.

Kammalawa:

Hoton da ake yadawa a kafafen sada zumunta na zamani dake nuna wata mata cikin jini nade a tutar Najeriya yake kuma ikirarin ankashe ta ne a harbe-harbe da jami’an tsaro sukayi Lekki Toll Gate karya ne!

Hoton an dauke shi ne a wani shirin fim da aka dauka a Akwa Ibom game da cikar Najeriya shekaru 60 da samun mulkin kai. Matar da ake cece-kuce akanta tananan a raye kuma cikin koshin lafiya.

CDD tana jan hankalin jama’a game da yada labaran da basu da tabbacin sahihancin su. Kuna iya aikowa CDD labaran da kuke shakku akansu dan tantance muku ta hanyar WhatsApp ko gajeren sako ta wannan lamba +2349062910568 ko a shafin Twitter a: @CDDWestAfrica ko @CDDWestAfrica_H

#AgujiYadaLabaranBogi

Center for Democracy and Development West Africa| CDD West Africa