Hoton Dake Nuna Ma’aikatar “Long Life and Prosperity” a Jahar Imo da aka Lika a Jikin Wata Motar Safa Hoto Ne Na Bogi!

Tushen Magana:

Wani hoto mai dauke da tambari ko rubuto da aka yishi a turance kamar haka: “Ministry of Long Life and Prosperity Imo State” ya yadu sosai a dandalin Twitter kuma an ci gaba da yada wannan hoto a shafin Twitter tun ranar 11 ga watan Disamban shekara ta 2020, wannan hoto wani mai anfani da shafin na Twitter mai adireshi “@RealOlaudah”. Banda shafin Twitter, an kara yada hoto a shafukan Facebook da WhatsApp.

Gaskiyar Magana:

Binciken CDD ya gano cewa babu wata ma’aikta mai suna “Ministry of Long Life and Prosperity” a jahar Imo kuma hoton anyi anfani da fasaha ne aka kirkireshi sannan aka lika a jikin motar. Kodayake lokacin tsohon gwamna Rochas Okorocha ya kirikiri wata ma’aikata mai suna “Ministry of Happiness” ma’ana ma’aikatar farin ciki, amma gwamnan jahar Imo na yanzu Hope Uzodinma ya soke wannan ma’aikatar.

Karin binciken da CDD ta aiwatar ta hanyar fasahar zamani ya gano cewa ainihin motar da aka likawa hoton ma’aikata hoto ne mallakin shafin yanar gizo na Anis Transport dake Bangkok.

CDD har wayau ta gano cewa anyi rubutun ne da manhajar “Photoshop”.

Hoton bogi da aka yada  
   Hoton na asali

                 

Wannan ba shine karo na farko da akayi anfani da hoton ba, shekaru uku da suka wuce, shafin yanar gizo da yayi kaurin suna wajen yada labarn bogi mai suna igberetvnews.com ya wallafa Just In!! Rochas Okorocha Of Imo State To Impose Commissioner For Long Life & Prosperity

Kammalawa:

Wani hoto da ake yadawa a shafukan sada zumunta na zamani dake nuna tambarin ma’aikatar “Ministry of Long Life and Prosperity Imo State” a jikin wata motar safa hoto ne wadda akayi anfani da manhajar “Photoshop” wajen sauya masa fasali, kuma an samo shi ne tun farko daga yanar gizo.

CDD tana jan hankalin jama’a da bayanai ko labarai bayanai marasa tushe ko sahihanci.

#AgujiYadaLabaranBogi