Hoton Dake Nuna Cewa Wassu Matasa Sun Kama Shugabannin Jam’iyyar APC Da Kudade a Owo Hoto Ne Na Bogi!

Tushen Magana:

Adaidai lokacin da zaben gwama a jahar Ondo ke cigaba da gudana ayau Asabat, 10 ga watan Oktoban shekara ta 2020, wani mutum mai suna , Ifedolapo Osun, (@DolapoOsun1414) ya wallafa wani hoto a shafin san a Twitter inda yace wassau matasa sun damke wassu shugabannin jam’iyyar APC da tarin kudade da yawan su yakai miliyoyin naira.

Hoton ya nuna wassu matasa guda biyu dauke da daurin kudade a tare dasu.

Anyiwa hoton wani jawabi kamar haka: “Asiri ya tonu game da zaben Ondo! Akerelodu da jam’iyyarsa ta APC zasu fadi a Owo saidai kuma wassu matasa yan kishin kasa sun kama shugabannnin jam’iyyar APC da kudade da yawan su yakai miliyoyin naira…”

Gaskiyar Magana:

Binciken da CDD ta aiwatar ya gano cewa hoton da ake yadawa din na karya dan bama a jahar Ondo aka daukeshi ba.

CDD har wayau ta gano cewa kafafen sadarwa na yanar gizo da yawa sunyi anfani da hoton.

Hakanan, rundanar yan sandan Najeriya reshen jahar Niger tayi anfani da  hoton a ranar 2 ga watan Oktoban shekara ta 2020 a shafin ta Facebook.

Har wayau gidan talabijin na AIT ma ya wallafa hoton  a ranar 3 ga watan Oktoban shekara ta 2020 a lokacin da yake labarta cewa rundunar yan sanda ta kama wassu mutane bisa zargin aikata laifuka daban-daban.

Kammalawa:

Hoton da ake yadawa a shafin Twitter cewa wassu matasa sun kama shugabannin jam’iyyar APC da tarin kudade da yawan su yakai miliyoyin naira hoto ne na bogi. Hoton da ake yadawa din ba’a jahar Ondo aka dauke shi ba.

#AgujiYadaLabaranBogi

Kuna iya aikowa CDD labarai ko bayanan da kuke da shakku akansu dan ta tantance muku sahihancin su. Zaku iya turo labaran ta wannan lamba: +2349062910568 ko a shafukan mu na Twitter a @CDDWestAfrica ko @CDDWestAfrica_H

Center for Democracy and Development West Africa| CDD West Africa