Har Yanzu Ba’a Nada Dr. Ngozi Okonjo-Iweala a Matsayin Mace Ta Farko Kuma Babbar Daraktar WTO Ba!

Tushen Magana:

A ranar Alhamis, 8 ga watan Oktoban shekara ta 2020, kafafen sada zumunta na zamani da dama sun rawaito cewa tsohuwar Ministar Kudi ta kasa Dr. Ngozi Okonj-Iweala ta zama mace ta farko da ta zama babbar daraktar hukumar cinikayya ta duniya wato World Trade Organization (WTO).

Majiyoyi da yawa musamman a Twitter da Facebook da WhatsApp sun wallafa labarin cewa an nada Dr. Iweala a matsayin babbar daraktar WTO.

Gaskiyar Magana:

Binciken da CDD ta gudanar ya gano cewa Dr. Ngozi Okonjo-Iweala takai matakin zamowa shugaban WTO din ne, ita da wata mata yar kasar Koriya ta Kudu mai suna Yoo Myoung Hee ne suka kai ga samun kansu a wannan mataki.

Jita-jiatr da ake yadawa cewa Okonjo-Iweala ta zama babbar daraktar WTO din karya ne. WTO har yanzu bata kammala zaben wanda zai jagorance ta ba.

A wata sanarwa da aka fitar wadda tayi bayani game da mata guda biyun da suka samu shiga matakin karshe na zabe, shugaban majalisar koli na WTO din Ambassador David Walker yace za’a fara tuntuba game da zaben a ranar 19 ga watan Oktoba kuma zai kai har ranar 27 ga Oktoban da muke ciki kafin agama

Walker yace za’ayi anfani da wa’adin dan tantance wadda ya kamata ya zama shugaban kungiyar kasuwanci ta duniyar.

Sanarwar tace: “a tsawon lokacin da za’a dauka ana tantance wanda ya kamata ya zama shugaban kungiyar cinikayya ta duniyar, za’a tambayi  mambobin kungiyar cikin sirri wanda sukeso ya jagoranci kungiyar, daga nan sai a zabo mutane biyu bayan tuntuba.Bayan haka sai wani sashi da ake kira troika ya gabatar da babban daraktan kungiyar a yanzu wanda suke bada shawarar ya zama sabon babban daraktan, shi kuma babban daraktan na yanzu zai jagoranci zama na babban azure dan gabatar musu shawarar troika wanda daga shi kuma sai nada sabon babban daraktan”

Dr. Ngozi Okonjo-Iweala itace yar takarar zama babbar daraktar kungiyar daga Najeriya kuma ta taba kasancewa Ministan kudi dama harkokin wajen Najeriya a baya. Har wayau ta taba kasancewa daraktar  ta bankin duniya.

Kammalawa:

Kawo ranar Alhamis, 8 ga watan Oktoban shekara ta 2020 ba’a nada Dr. Ngozi Okonjo-Iweala a matsayin babbar daraktar kungiyar cinikayya ta duniya ba, labaran da ake yadawa musamman a kafafen sada zumunta na zamani cewa ta zama babbar daraktar kungiyar bai tabbata ba tukunna.

Kungiyar cinikayya ta duniyar hanyanzu bata kai ga zaban wanda zai jagorance ta ba tukunna.

Summary:

Tantancewar Da CDD Ta Aiwatar

Har Yanzu Ba’a Nada Dr. Ngozi Okonjo-Iweala a Matsayin Mace Ta Farko Kuma Babbar Daraktar WTO Ba!

Kawo ranar Alhamis, 8 ga watan Oktoban shekara ta 2020 ba’a nada Dr. Ngozi Okonjo-Iweala a matsayin babbar daraktar kungiyar cinikayya ta duniya ba, labaran da ake yadawa musamman a kafafen sada zumunta na zamani cewa ta zama babbar daraktar kungiyar bai tabbata ba tukunna.

Kungiyar cinikayya ta duniyar hanyanzu bata kai ga zaban wanda zai jagorance ta ba tukunna.

Kuna iya aikowa CDD labarai ko bayanan da kuke da shakku akansu dan ta tantance muku sahihancin su. Zaku iya turo labaran ta wannan lamba: +2349062910568 ko a shafukan mu na Twitter a @CDDWestAfrica ko @CDDWestAfrica_H

Center for Democracy and Development West Africa| CDD West Africa