Skip to main content

Gwamnatin Tarayya Bata Sanar Da 1 Ga Watan Yunin Shekara Ta 2020 ba Matasayin Ranar Komawa Makaranta Fadin Kasa

Tushen Magana:

A ranar 7 ga watan Afirilun shekara ta 2020 masu tantance sahihancin labarai na Cibiyar Bunkasa Demokaradiyya da Cigaba sun gano wassu rahotanni da dake yawo a yanar gizo suna ikirarin cewa gwamnatin tarayya ta sanar da ranar 1 ga watan Yunin shekara ta 2020 a matsayin ranar da jami’o’i da kwalejojin fasaha a fadin kasa zasu bude domin cigaba da karatu.

Gaskiyar Magana:

A watan Maris din shekara ta 2020 ne ma’aikatar lafiya ta kasa ta bada umarnin rufe dukkan makarantu a fadin Najeriya baki daya sakamakon tabbatar bullar cutar Corona. Ma’aikatar ilimin ta bayyana cewa rufe makarantun daya ne daga cikin matakan kare yaduwar cutar Corona.

Tantancewar da CDD ta aiwatar ta gano cewa duk rahotannin da aka yada gdin sun dogara ne da dalilin cewa an rufe makarantu a watan Maris sukayi hasashen bude makarantun a ranar 1 ga watan Yunin shekara ta 2020.

Idan za’a iya tunawa dai Mr. Sonny Echono a madadin babbabn sakatare g minitsan ilimi Malam Adamu Adamu ya bada umarnin rufe makarantun jaddada hadin kai gud 104 a fadin kasa baki daya kafin ranar 26 ga watan Maris ko kafin haka na tsawon wata guda saboda fuskantar annobar cutar Corona.

Har wayau CDD ta gano cewa duk rahotannin da suka bada sanarwar bude makarantun sun gaza danganta labaran nasu da wanda ya fadi labarin, da yawa daga cikin rahotonnin sunyi anfani ne da hotunan Shugaba Muhammadu Buhari ba tare da danganta labarin dashi ba.

Ma’aikatar ilimin a ranar 23 ga watan Afirilun shekara ta 2020 ta maida martani game labarin bude makarantun inda ta bayyana labarin a matsayin na bogi. Karamin Ministan ilimi  Chukwuemeka Nwajiuba yayi bayani a wani taron manema labarai a babban birnin tarayya Abuja inda yace har yanzu ba’a saka ranar dawowa makarantar ba.

Nwajiuba yace gwamnatin tarayya baza ta jefa rayuwar yan makaranta bat a hanyar bude makarantu ba tare da nazari ba. “Shugaban kasa yana ta kokarin saita tattalin arziki sannu a hankali, in angama wannan za’a bude makarantu, amma yanzu baza muyi saurin sanar mutane lokacin bude makarantun ba”, inji Nwajiuba.

A lokacin da yake sassauta doka hana fita a jihohin Lagos, Osun da babban birnin tarayya Abuja, Shugaba Buhari ya bayyana cewa makarantu zasu cigaba da kasancewa a rufe a fadin kasa baki daya har sai angama nazari akansu, Buhari  ya shawarci hukumomin makarantu da su cigaba gabatar da koyo da koyarwa ta hanyar yanar gizo.

Binciken da CDD ta gudanar a shafin yanar gizo na ma’aitakar ilimin ta tayrayya ya nuna cewa ma’aikatar bata fitar wata sanarwar ba game da bude makarantu ba.

Hasalima ma’aikatar ilimin ta wallafa wani jawabi a shafin tan a Facebook inda ta nesanta kanta da sanarwar da akea yada cewa ta bada umarnin bude makarantu, ga abinda ma’aikatar ta wallafa, “Kuyi hankali da labaran bogi!!! Har yanzu babu kayyadajjiyar ranar komawa makaranta, muna kira ga mutane da suyi watsi da sanarwar dake yawo. Kuyi watsi wannan sanarwa”

Kammalawa:

Har yanzu gwamnatin tarayya bata tsaida ranar bude makarantu dake fadin kasarnan ba. CDD tana shawartan iyaye, makarantu dama dalibai da suyi watsi da jita-jitar zaurukan yanar gizo da kafafan sada zumunta na zamani ke yadawa cewa za’a koma makaranta a ranar 1 ga watan Yunin shekara ta 2020

Leave a Reply