Gwamnatin Tarayya Ba Ta Saye Manhajar WhatsApp Ba

Tushen Magana:

A ranar 10 ga watan Maris din shekara ta 2021, masu bin diddigin labarai dan gano sahihancin sun a Cibiyar Bunkasa Demokaradiyya da Cigaba (CDD) sun gano wani sako da aka wallafa a shafin Facebook da ke ikirarin cewa gwamnatin tarayyar Najeriya ta saye manhajar WhatsApp da ake amfani da ita wajen turawa da karbar sakonni.

Sakon da aka wallafa din ya bayyana cewa gwamnatin tarayya ta saye manhajar ne akan kimanin kudi biliyan uku (kodayake ba a bayyana biliyan ukun na nau’in wane kudi bane).

Sakon ya kara da cewa masu amfani da manhajar su gaggauta barin amfani da ita dan komawa yin amfani “Signal App” saboda a cewar sakon gwamnatin Najeriya za ta ci gaba das aka ido akan abinda mutane ke yi a manhajar ta WhatsApp.

Wani bangare na sakon yace: “Za a rika bin diddigin abinda kake yi! Daina amfani da WhatsApp yanzu-yanzu! Fara yin amfani da Signal App yanzu! Signal App baya bada damar sa ido akan abinda kakeyi”

Gaskiyar Magana:

Binciken da CDD ta aiwatar ya gano cewa gwamnatin Najeriya ba ta saye manhajar WhwatsAppm din ba kamara yadda akayi ikirari.

Karin binciken da CDD ta aiwatar ya gano cewa sakon da wanda wani mai lura da wani shafin Facebook mai suna “Best of Mazi Nnamdi Kanu”  ya wallafa shi dandalin Facebook din ya riga ya aiyana shi a matsayin labarin bogi.

Shafin Facebook a martanin da ya mayar game da sakon bogin da aka wallafa din yace tuni wasu masu tantance sahihancin bayanai masu zaman kansu sun tantance shi kuma sun gano cewa karya ne.

Wani karin binciken da zurfafa ya gano cewa, kamfanin sada zumunta da muhawarar na Facebook a martanin day a mayarwa kamfanin dillancin labarai na AFP ya bayyana sakon a matsayin na karya.

Ba zai yiwu Facebook su sayar da kamfanin da ta samar dashi akan zabar kudi dala biliyan goma sha tara da digo uku ($19.3 billion), da ke da mallakar hannun jari da kudin su yakai dala biliyan sha biyu ($12 billion), abu ne da bazai yiwu ba ace an sayar dashi akan naira biliyan uku (3BN)  kacal ga gwamnatin Najeriya.

Yana da kyau a sani cewa a halin yanzu idan za a sayar da WhatsApp zai kai tsabar kudi dala biliyan dari biyar ($500 billion), dan haka babu ta yadda za a sayar dashi a naira biliyan uku kacal.

Alamu na nuna cewa wanda ya wallafa sakon ka iya zama masoyi ga Nnamdi Kanu, mai fafutukar neman kirikiro kasar Biafra wadda magoya bayan suka kware wajen yada labaran karya.

Kammalawa:

Bayan gudanar da zuzzurfan bincike, CDD na tabbatar da cewa gwamnatin Najeirya ba ta saye manhajar WhatsApp ba kamar yadda wani sakon da aka yada a wasu shafukan sada zumunta na zamani ya bayyana.

CDD na jan hankalin jama’a game da yin nazari da tantance sahihancin sakonni da labarai kafin yada su ga sauran jama’a.

Kuna iya aikowa CDD labaran da kuke da shakku akansu da gano muku gaskiyar su. Za ku iya turo gajeren sako (SMS) ta manhajar WhastApp akan lamba: +2349062910568 ko ku tuntube mu a shafin Twitter a @CDDWestAfrica.

#AgujiYadaLabaranBogi

Center for Democracy and Development West Africa| CDD West Africa