Skip to main content

Tushen Magana:

Masu tantance sahihancin labarai na Cibiyar Bunkasa Demokarardiyya Da Cigaba (CDD) a ranar Alhamis, 23 ga watan Afirilun shekara ta 2020 din da ta gabata ne suka gano wata sanarwa da ake yadawa cewa gwamnatin Jahar Legas ta wallafa sunayen wassu cibiyoyin lafiya da sukayi mu’amila da masu dauke da Cutar Corona.

Wannan sanarwa da aka yada ta sosai ta manhajar WhatsApp tana dauke sunayen asibitoci guda goma sha bakwai (17) dake Jahar Legas din.

Gaskiyar Magana:

Binciken da CDD ta aiwatar ya gano cewa gwamnatin jahar Legas bata fitar da kowace sanarwa dake dauke suneyen asibitoci ko cibiyoyin lafiya guda goma sha bakwai ba (17). Hasali ma, a lokacin da yake yiwa yan jarida jawabi a ranar Ladi 19 ga watan Afirilun shekara ta 2020, kwamishinan lafiya na jahar Legas din, Farfesa Akin Abayomi ya bayyana cewa asibitoci goma sha bakwai (17) sun bukaci ma’aikatar lafiyar data tallafa musu sakamakon ziyartar su da masu dauke da Cutar Corona sukayi, amma kwamishinan bai bayyana sunayen asibitocin ba.

Kwanaki kadan bayan jawabin kwamishinan sai wata sanarwa mai dauke da sunayen asibitoci masu zaman kansu guda goma sha bakwai (17) ta fara yaduwa a yanar gizo.

A martanin ta game da sanarwar bogin da aka yada mai dauke sunayen asibitoci masu zaman kansu goma sha bakwai (17) din, gwamnatin Jahar Legas ta bukaci mutane da suyi watsi da sanarwar saboda rashin tushen ta.

Abiola Idowu wanda shine sakatare a ma’aikatar lafiyar ya tabbatar da cewa sanarwar bata fito daga gwamnatin Legas din.

Mr. Idowu ya tabbatar da cewa wassu asibitoci sun bada kulawa ga wassu masu dauke da Cutar Corona. Mr. Idowu yaja hankalin mutane da su guji yada kyama ga asibitoci ko mutanen da suka kamu cutar Corona.

Har wayau a wani jawabi data walafa a shfinta na Twitter, ma’aikatar lafiyar ta jahar Legas ta gargadi asibitoci dama cibiyoyin lafiya a jahar dasu guji karba ko bada kulawa ga masu dauke da cutar COVID-19 ba tare da izini ba. Kamar yadda jawabin ya bayyana, duk wani asibiti ko cibiyar lafiya da aka samu da karya wannan doka zai hadu da hukunci.

Kammalawa:

Gwamnatin jahar Legas bata wallafa sunayen asibitoci goma sha bakwai (17) da sukayi bada kulawa ga masu dauke da cutar Corona ba. CDD tana jan hankalin mutane da suyi nesa da yada labarin da ka’iya haifar fargaba ko tarnaki ga kokarin yakar cutar Corona.

#AdainaYadaLabaranKarya

Leave a Reply