Gwamnatin Jahar Katsina Bata Hana Anfani Da Facebook da WhatsApp Ba!

Tushen Magana:

A ranar Laraba, 9 ga watan Disamban shekara ta 2020, masu tantance sahihancin labarai na Cibiyar Bunkasa Demokaradiyya da Cigaba (CDD) sun gano wani labari da aka wallafa kuma ya yadu kamar wutar daji, labarin yace gwamnatin jahar Katsina ta haramta anfani da kafafen sada zumunta na zamani wato Facebook da WhatsApp.

Labarin wadda majiyoyi masu tarin yawa da suka hada da: Katsina government bans WhatsApp in schools, prohibits Facebook amongst workers;, Katsina bans WhatsApp usage in public schools; Katsina government bans WhatsApp in schools, bars staff from commenting negatively or positively on government activities on Facebook suka wallafi yace an hana ma’aikata da daliban jahar Katsina daga anfani da Facebook da WhatsApp.

Gaskiyar Magana:

Binciken da CDD ta gudanar ya gano cewa gwamnatin jahar Katsina bata hana dalibai da ma’aikatan jahar yin anfani da WhatsApp da Facebook ba.

Da yake yiwa CDD Karin bayani akan batun, kwamishinan ilimi na jahar Katsina, Farfesa Badamasi Lawal yace, ba kamar yadda ake yayatawa ba, gwamnatin Katsina bata hana anfani da kafafen sada zumunta na zamani ba, abinda kawai tayi shine dakatar da yin anfani da “zauren WhatsApp” da malaman makarantu ke anfani dashi wajen harkar sadarwa bayan daya daga cikin zaurukan ya janyo cece-kuce.

Farfesa Lawal yace wani sakon WhatsApp ne da wani malami ya rubuta a daya daga cikin zaurukan tattaunawa tsakanin malamai ya janyo musayan maganganu da suka kawo rashin jituwa tsakanin wani shugaban makaranta da wani malami.

Acewar kwamishinan ilimin, daraktocin shiyya-shiyya ne suka samar da Zaurukan WhatsApp din dan saukaka yadda malaman zasu rika tattaunawa da junan su akan al’amuran aiki amma tunda suna haifar da rashin jituwa sai aka dauki matakin dakatar dasu.

Farfesa Lawal yace: “babu wanda ya hana kowane mamali anfani da WhatsApp, abinda kawai aka dakatar shine “zauren WhatsApp (WhatsApp group)” da malaman ke anfani dashi”.

“labarin da aketa yadawa cewa gwamnatin jahar Katsina ta hana ma’aikata yin anfai da WhatsApp da Facebook karya ne”- Farfesa Badamasi Lawal.

Kammalawa:

Labarin da ake yadawa cewa gwamnatin jahar Katsina ta hana ma’aikata da malaman makarantu yin anfani da WhastApp da Facebook karya ne. kwamishinan ilimin jahar ta Katsina ya tabbatar da cewa abinda kawai aka dakatar shine “WhatsApp group” da malaman makarantu ke anfani dashi dan saukaka tattaunawa a tsakanin su bayan rigima ta faru tsakanin wani malami da shugaban makaranta acikin daya daga cikin zaurukan tattaunawar (WhatsApp groups).

CDD na jan hankalin jama’a game yada labaran da basu tantance sahihancin su ba.

Kuna iya aikowa CDD labaran da kuke shakku akansu dan tantance muku ta hanyar WhatsApp ko gajeren sako ta wannan lamba +2349062910568 ko a shafin Twitter a: @CDDWestAfrica ko @CDDWestAfrica_H

#AgujiYadaLabaranBogi

Center for Democracy and Development West Africa| CDD West Africa