Gwamnatin Jahar Kano Ba Ta Rushe Makarantar Sheikh Abduljabbar Ba!

Tushen Magana:

A ranar Asabat, 6 ga watan Fabrairun shekara ta 2021, masu bin diddigin sahihancin labarai na Cibiyar Bunkasa Demokaradiyya da Cigaba (CDD) sun gano wani labari da BBC Hausa sunka wallafa cewa gwamnatin Kano ta rushe makarantar Sheikh Abduljabbar Nasiru Kabara.

Wasu kafafen yada labarai da yawa tare da tashoshin kallo na dandalin YouTube duk wallafa wannan labari. Majiyoyin sun hada da: Express Radio Kano, Legit Hausa, Kadaura 24, tashoshin YouTube da suka buga labarin sun hada da: 9ja Hausa TV, Action Hausa TV, Alheri Royal TV, Kundin Labarai TV, Komai Da Ruwan Ka TV 1

Labarin yayi ikirarin cewa daukar hukuncin rushe makarantar malamin ya biyo bayan hana shi wa’azi da gwamnatin tayi ne sakamakon cece-kucen da maganganu sa suka janyo a tsakanin Musulmai tare da yin maganganu na batanci ga Musulunci.

Gaskiyar Magana:

Binciken da CDD ta gudanar ya gano cewa gwamnatin jahar Kano ba ta rushe makarantar malamin ba kamar yadda labarai da dama da kafafen yada labarai suka wallafa suka bayyana.

Ziyarar gani da ido da wakilin CDD yakai inda makaranta da gidan malamin suke ta gano cewa babu abinda ya samu maranta ko masallacin malamin. Dan haka labarin cewa an rushe makarantar malamin karya ne.

Karin binciken da CDD ta gudanar ya gano gine-ginen da aka rushen din suna tazarar akalla mita dari biyu da makaranta da masallacin malamin.

Gine-ginen da aka rushen din sun kunshi gidaje ne da sauran muhallai da mutane daban-daban suka gina wanda a cewar hukumar kula da tsara gine-gine ta jahar Kano (KNUPDA) tace ba a yisu akan ka’ida ba.

Anga yan sanda cikin shiri a motoci na zagaye da gidan malamin yayin da yara ke ci gaba da wasa cikin baraguzan rusau din da aka yi a filin da ke da tazara daga gidan malamin.

Da yake magana da wakilin CDD, darakta mai kula tsara birane na hukumar KNUPDA, Rilwanu Baita y ace labarin cewa an rushe makarantar Abduljabbar labari ne bogi.

Baita ya kara da cewa KNUPDA ba ta rushe makaranta ko wata kadara ta malamin ba, hasalima abinda ya faru shine rushe gine-gine da aka yisu ba bisa ka’ida ba a wani waje da ake kira Filin Mushe.

Baita yace: “KNUPDA ta gano wasu gine-gine da wasu mutane suka yi a Filin Mushe da ke karamar hukumar Gwale, dan haka sai ta aikawa wadan da suka yi gargadin karya ka’ida da suka yi tun watannin baya amma sai suka yi watsi da sanarwar, saboda haka KNUPDA ta rushe su sakamakon saba ka’ida da kuma kunnen uwar shegu da sanarwar da aka baiwa mutane cewa su dakatar da gine-gine”

“duk mutane da suka yi gine-gine a wannan waje basu takardun izini, kuma doka ta bamu ikon ruguje duk wani gini da aka yishi ba bisa ka’ida ba”

“ina kara jaddada cewa ba makaranta KNUPDA ta rushe ba face gine-gine da aka yisu cikin rashin izini”

Kammalawa:

Labarin da kafafen da yada labarai da yawa suka wallafa cewa gwamnatin jahar Kano ta rushe makarantar Sheikh Abduljabbar karya ne.

Ziyarar da CDD takai wurin da akayi rusau din da karin binciken da ta gudanar ya gano babu abinda ya samu makaranta ko masallacin malamin.

CDD na tabbatar da cewa wannan labari ne na bogi dan haka jama’a suyi watsi dashi.

CDD na jan hankalin kafafen yada labarai da jama’a da su guji yada labaran karya ko wadan da basu da tabbacin sahihancin su.

Kuna iya aikowa CDD labaran da kuke da shakku akansu dan tantance muku gaskiyar su ta hanyar aiko gajeren sako ko ta manhajar WhatsApp akan lamba: +2349062910568

#AgujiYadaLabaranBogi

Center for Democracy and Development West Africa| CDD West Africa