Skip to main content

Tushen Magana:

A ranar 11 ga watan Mayun shekara ta 2020, wani zauren yanar gizo ya wallafa wani labarai da yayi masa take kamar haka: “Labari da dumi-duminsa! Gwamnan Sokoto ya mutu”

Labarin yna dauke da hoto Gwamna Aminu Waziri Tambuwal na Jahar Sokoto kuma ya bayyana cewa Tambuwal din ya mutu.

Gaskiyar Magana:

Binciken da CDD ta aiwatar ya gano cewa Gwamna Aminu Waziri Tambuwal yanan a raye. Binciken masu tantance sahihancin labari na CDD din ya kara gano cewa gundarin labarin ya nuna cewa Gwmnan Jahar Sokoto na farar hula na biyu wato Dr. Garba Nadama shine ya rasu a ranar 4 ga watan Mayun 2020.

Labarin wanda aka karanta shi sama da sau 38,000 wanda suka rubuta shi sun tsarashi dan da nufin jan hankalin mutane dan su karanta shi kuma su ziyarci shafin u na yanar gizo.

Gwamnan Jahar Sokoto a halin yanzu wato Aminu Waziri Tambuwal shine ya sanar da rasuwar tsohon gwamnan inda ya bayyana alhini da jimamin sa game rashin.

Tambuwal ya bayyana ta’aziyyarsa ga iyalan marigayi Garba bisa rashin da jahar Sokoton tayi na rashin babban dan siyasar.

Acikin labarin, majiyar ta rawaito labarin inda ta bayyana rasuwar marigayi Garba kuma tace Gwamna Tambuwal ne ya sanar rasuwar a madadin gwamnatin Jahar Sokoto amma sai sukayi anfani da jikitaccen jigon labari dama hoton Gwamnan dake mulki yanzu.

Har wayau bincikene CDD ya gani cewa zauren yanar gizon day a wallafa labarin mai suna www|dot|UniqueMusic|dot|com|ng an samar dashi ne wallafa wakoki amma ya bige wallafa labarai kuma yana anfani da wani tsari da ake kira “clickbait” a turance dan jan hankalin mutane su ziyarci shafin.

Shin me ake nufi da tsarin clickbait?

Clickbait wani salo da mazanbata ke anfani dashi ta hanyar yin anfani da wani adireshin shafin yanar gizo da masu wallafi labarai ke anfani dashi dan jan hankalin mutane su zitarci shafin su. Akasari masu wallafa labarai a zaurukan yanar gizo ne ke anfani dashi saboda karawa kansu yawan masu ziyartan shafin su.

Kammalawa:

Gwamna Aminu Waziri Tambuwal yana nan a raye. CDD tana jan hankalin mutane da su rika karanta gundarin labari dan tantance shi kafin yadashi musamman idan labarin ya fito daga zauren yada gulmace-gulmace dake gina jigon labari mai daukar hankali.

Leave a Reply