Skip to main content

FUNAM Bata Ce Keda Alhakin Kona Ababen Hawan Masu Zanga-Zangar #EndSARS a Abuja Ba

Tushen Magana:

A ranar Talata, 20 ga watan Oktoban shekara ta 2020, anga wani jawabi dake cewa wata kungiyar Fulani mai suna Fulani Nationality Movement (FUNAM) a turance ta bayyana cewa itace takai hari akan masu zanga-zangar #EndSARS a yankin Apo dake Abuja.

Kamar yadda jawabin ya bayyana, kungiyar zata cigaba da kai hari akan masu zanga-zangar ranar Laraba, 21 ga watan Oktoban shekara ta 2020.

Sanarwar tace: “muna bada umarni ga dukkan ya’yan kungiyar mu su shirya dan shiga cikin yakin da muka dade muna jira”.

Gaskiyar Magana:

Binciken da CDD ta gudanar yabi asalin inda sanarwar ta fita kuma ya gano cewa wani shafin bogi da akayiwa lakabi da Jungle Journalist ne ya fara wallafa sanarwar inda kuma wani zauren yanar gizo mai suna Nairaland shima ya wallafa, hakanan an kara wallafa wannan jawabi a dandanlin WhatsApp da Facebook dama Twitter.

Karin bincike da CDD ta gudanar a gano cewa FUNAM wata kungiya ce da aka samar wadda bata da sanannun mambobi ko shuwagabanni a shekara ta 2018. A wancan lokaci wannan kungiya da ba’a san ya’ya ko mambobin ta ba ta dauki alhakin kai hare-haren da aka aiwatar akan rikicin makiyaya da manoma.

Wannan kungiya bincike ya tabbatar da cewa kungiya c eta bogi wadda ake anfani da ita dan ingiza wutar tashin hankali mai alaka da kabilanci tun kimanin shekaru uku da suka gabata. Kuma wadan da suka samar da ita na kokarin haifar da tashin hankalin kabilanci ne shi yasa sukace kungiyar ce takai hari akan masu zanga-zanga a yankin Apo a ranar 19 ga watan Oktoban shekara ta 2020.

Kammalawa:

Kungiyar da ake kira FUNAM kungiya ce ta bogi kuma an alakanta da harin da aka kaiwa masu zanga-zangar #EndSARS a yankin Apo dake babban birnin tarayya Abuja ne dan ingiza tsana da rura wutar tashin hankalin kabilanci.

Anyi anfani da kungiyar ne dan a kanbama tashin hankali, saboda haka CDD ke jan hankali jama’a da cewa suyi watsi da sanarwar kungiyar.

#AgujiYadaLabaranBogi

Kuna iya aikowa CDD labarai ko bayanan da kuke da shakku akansu dan ta tantance muku sahihancin su. Zaku iya turo labaran ta wannan lamba: +2349062910568 ko a shafukan mu na Twitter a @CDDWestAfrica ko @CDDWestAfrica_H

Center for Democracy and Development West Africa| CDD West Africa