Skip to main content

Femi Adesina Bai Bayyana Zanga-Zangar Neman Dakatar Da Yan Sandan SARS A Matsayin Shiririta Ba

Tushen Magana:

A ranar Laraba, 14 ga watan Oktoban shekara ta 2020, masu tantance sahihancin labarai na Cibiyar Bunkasa Demokaradiyya Da Cigaba (CDD) sun gano yadda shafin bayyana ra’ayi da musayan bayanai na Twitter ya zama dandalin cece-kuce game da wata magana da aka danganta ta da mai baiwa shugaban kasa shawara ta fuskara yada labarai Femi Adesina.

Maganar da ta zama abin tattaunawa a wannan rana ta alakanta Mr. Adesina da bayyana zanga-zangar da yan matasan Najeriya keyi dan neman gwamnati ta dakatar day an sandan SARS da cewa shiririta ce.

Acikin wani bidiyon mai tsawon minti biyu da dakika biyu da aka yada a shafin na Twitter mai dauke da tambarin gidan talabijin na Channels Adesina yace shi anasa nazarin zanga-zangar da akeyi dan neman ruguza yan sandan SARS ba wani abu bane illa almara da shiririta mai cike da ban dariya.

Gaskiyar Magana:

Binciken da CDD ta gudanar game da batun bidiyon Adesinan ya gano cewa bidiyon da ake yadawa yanzu tsohon bidiyo ne kuma bashi da alaka da zanga-zangar kin jinin yan sandan SARS.

Hirar da ake zargen Adesina yayi da gidan talabijin na Channels din an dauke ta ne ranar 6 ga watan Agustan da ya gabata lokacin da ake gudanar da zanga-zangar neman juyin-juya hali ta #RevolutionNow.

Wani Karin binciken da CDD ta aiwatar ya gano cewa bidiyon da ake yadawa din an sauya masa fasali ne dan karkata fahimtar mutane zuwa yarda da cewa anyi hirar ne a ranar Laraba, 14 ga watan Oktoban da muke ciki.

Kammalawa:

Bidiyon da ake yadawa cewa mai magana da yawun shugaban kasa, Femi Adesina ya suffanta zanga-zangar da yan Najeriya keyi dan neman ruguza yan sandan SARS a matsayin wasan yara bidiyo ne na bogi.

Binciken CDD ya gano cewa asalin bidiyon da ake yadawa din an dauke shi ne a ranar 6 ga watan Agustan da ya gabata inda Adesinan yayi magana game zanga-zangar neman juyin-juya hali ta #RevolutionNow amma sai aka sauya masa fasali dan alakanta shi da zanga-zangar #EndSARS dake faruwa yanzu.

#AgujiYadaLabaranKarya

Kuna iya aikowa CDD labarai ko bayanan da kuke da shakku akansu dan ta tantance muku sahihancin su. Zaku iya turo labaran ta wannan lamba: +2349062910568 ko a shafukan mu na Twitter a @CDDWestAfrica ko @CDDWestAfrica_H

Center for Democracy and Development West Africa| CDD West Africa