Farfesa Ibrahim Gambari Baiyi Murabus Daga Kujerar Sa Ta Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Kasa Ba

Tushen Magana:

A ranar Talata, 19 ga watan Mayun shekara ta 2020, dayawa daga cikin kafafen yada labaran na yanar gizo sun wallafa wani labari dake cewa, Farfesa Ibrahim Gambari, shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa yayi murabus daga mukamin sa. Agina jigon labarin kamar haka: “Shugaban ma’aikatan Fadar Shugaban Kasa, Farfesa Ibrahim Gambari yayi murabus

Gaskiyar Magana:

Shugaba Muhammadu Buhari ya nada Farfesa Ibrahim Gambari ne a matsayin shugaban ma’aikatan fadar sa tun bayan rasuwar marigayi Abba Kyari bayan da ya kamu da cutar Corona.

Sakataren gwamnatin tarayya, Boss Mustapha ne ya sanar da nadin Farfesa Gambari a matsayin shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa Muhammadu Buhari a ranar 13 ga watan Mayun shekara ta 2020.

Ba kamar yadda sanarwar nadin Farfesa Gambarin da Boss Mustapha ya sanar ba, labaran da aka wallafa sun jirkita fahimtar mutane game da labarin inda suka bayyana murabus din shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasar.

Kodayake anata cece-kuce game da labarin murabus din Farfesa Gambarin, tantancewar da CDD ta aiwatar ta gano cewa Gambari yana daram akan mukamin sa.

Akwai rahotannin da aka wallafa da suka bayyana murabus din Farfesa Ibrahim Gambari daga jagorancin kungiyar farar hula mai suna Savannah Centre for Diplomacy, Democracy and Development (SCDDD), gaskiya ne Farfesa Gambari ya sauka daga jagorancin wannan kungiyar farar hula.

Bayanin murabus din Farfesa Gambarin daga kungiyar farar hular yana kunshe ne acikin sanarwar da babban daraktan kungiyar, Ambasada Abdullahi Omaki ya sanyawa hannu a ranar Talata, 19 ga watan Mayun shekara ta 2020.

Kammalawa:

Farfesa Ibrahim Gambari baiyi murabus daga mukamin sa na shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa ba. Saidai Farfesa Gambarin ya sauka ne daga mukamin sa na shugaban kungiyar farar hula mai lakabin SCDDD.

CDD tana jan hankalin jama’a da su rika karanta gundarin labari ba kawai su karanta jigon sa saboda jigon labari na iya jirkita fahimtar mai karatu akan ainihin abinda labari ya kunsa.

Kuna iya turo wa CDD sakonni da labaran da kuke da shakku akansu dan tantance sahihancin su ta wannan lamba: +2349062910568 ko ku tuntunbe mu a shafin mu na Twitter mai adireshi kamar haka: @CDDWestAfrica_H.

Leave a Comment

Your email address will not be published.